✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu da Shettima sun kashe N5bn a tafiye-tafiye cikin watanni uku

Duk wata tafiya, in dai ba wata fa’ida za ta kawo ga al’umma kasa ba, sai a yi watsi da ita.

Shugaban Kasa Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima da Uwargidan Shugaban Kasa, Remi Tinubu, sun kashe fiye da Naira biliyan 5.24 wajen tafiye-tafiye a cikin gida da kasashen waje, a tsakanin watan Janairu zuwa Maris din 2024.

Hakan na cikin wani bincike kan kudaden tafiye-tafiye ta hanyar amfani da wata kafar fasaha mai suna GovSpend da ke bin diddigin abin da Gwamnatin Tarayya ta kashe, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Binciken ya nuna cewa, an kashe Naira biliyan 1.35 a matsayin kudaden tafiye-tafiyen Shugaban Kasa da sauran abubuwan da suka danganci haka a cikin wata uku, sannan aka kashe Naira biliyan 3.53 wajen musayar kudaden kasashen waje.

Sai kuma Naira miliyan 637.85 da aka bayar ga hukumomin shirya tafiye-tafiyen, domin sayen tikitin jirgi ga Shugaban Kasar.

An biya wadannan kudade ne ta asusun ajiyar kuɗi na gidan gwamnati, sai dai wannan adadi bai kunshi na ayarin Shugaban Kasa ba.

Haka kuma, baya ga wannan adadi, gwamnati ta kashe Naira biliyan 12.59 wajen kula da jiragen saman Shugaban Kasa.

Shugaban Kasa ya kashe Naira biliyan 3.4 a kan tafiye-tafiye cikin wata shida na hawa mulkinsa.

Wannan adadi ya nuna an samu karin kashi 36 cikin 100 a kan Naira biliyan 2.49 da aka ware don tafiyetafiyen Shugaban Kasa a kasafin kudin bara.

An kashe jimillar Naira biliyan 8.64 a tafiye-tafiyen cikin gida da kasashen waje a tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Maris 2024.

Rahoton ya kuma nuna cewa, shugaban ya samu alawus na Naira miliyan 650.

Al’ummar kasa dai na nuna damuwarsu kan yawan tafiyetafiyen Shugaban Kasar, inda suka yi kira a tabbata kwalliya tana biya kudin sabulu daga tafiye-tafiye da yake yi.

A cikin wata bakwai na farko a karagar mulki, Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Shettima, sun ziyarci kasashe 16, tare da shafe kwana 91 a kasashen waje.

Bincike ya nuna cewa, kawo yanzu Tinubu ya ziyarci birnin Paris na kasar Faransa sau biyu, sai Landan da Guinea-Bissau sau biyu, Kenya, Jamhuriyar Benin, New Delhi a Indiya, Abu Dhabi da Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, sai Birnin New York na Amurka da Saudiyya da Berlin na kasar Jamus, inda duka ya kwashe kwana 55.

Shi kuma Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilci Shugaban Kasar a Italiya, Rasha, Afirka ta Kudu, Kyuba, China da Amurka, inda ya shafe kwana 36 a kasashen waje a 2023.

Da yake mayar da martani, wani kwararre kan harkokin kudi, Mista Olorunfemi Idris ya ce, tafiyetafiyen Shugaban Kasa na iya karfafa huldar diflomasiyya da inganta muradun kasa da kuma jawo masu zuba jari daga kasashen waje.

Misali tafiye-tafiyen da Shugaba Tinubu ya yi a baya-bayan nan sun haifar da samar da yarjejeniyar tsaro da bunkasar tattalin arziki da sauyin yanayi da kuma zuba jari a ayyukan samar da makamashi.

“Tafiyar Shugaban Kasa na kara inganta dangantaka da sauran kasashe, inda za ta haifar da kara samun hadin gwiwa a fanoni da dama.

“Shugaban Kasa na iya bayar da shawarwari ga muradun ci-gaban Nijeriya da tabbatar da yarjejeniyar hadin kan kasa,” in ji shi.

Duk da haka, Idris ya yi nuni da irin tsadar wadannan tafiyetafiye, wadanda za su iya karkatar da kudaden da ya kamata a aiwatar da wasu muhimman ayyuka, kamar kiwon lafiya da samar da ilimi da samar da ababen more rayuwa.

Naira biliyan 8.64 da aka kashe a tafiye-tafiyen Shugaba Tinubu a cikin wata takwas kadai, za a iya yin amfani da su wajen inganta kiwon lafiya da bunkasa ilimi ko samar da ababen more rayuwa.

Wani Farfesa a fannin Tattalin Arziki, Mista Cletus Agu ya ce, abin da ya kamata a lura da shi, shi ne, ko da an kashe kudaden ne ta hanyar da ta dace ko a’a, babu laifi, musamman idan hakan zai yi tasiri ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

Ya ce, “Abin da ya kamata a tambaya shi ne me ya sa yake kashe irin wadannan makudan kudaden? Mene ne amfani da kuma manufar yin haka?

“Za a iya kashe Naira miliyan 10, amma tasirin da hakan zai haifar ga bunkasa tattalin arzikin zai iya kai Naira miliyan 100.

“Amma idan tafiyar ta kashin kai ce daga wannan wuri zuwa wancan, hakan zai yi illa sosai saboda mutane suna shan wahala a yanzu.

“Amma idan ya kashe kudin ne da nufin inganta rayuwar al’ummar kasa da burinsa na inganta tattalin arzikin kasa, babu wani laifi a ciki.

Har ila yau, wani masanin tattalin arziki, Dokta Akin Akinleye, ya yi kira ga gwamnati ta rage yawan kudaden da take kashewa, wadanda ba su dace ba, lura da halin matsin tattalin arziki da kasar nan ke ciki.

Ya ce, “Suna da ’yancin yin tafiye-tafiye, amma dole ne su bai wa tattalin arzikin kasa fifiko, domin halin da tattalin arzikin kasa yake ciki ya yi muni.

“Suna kwasar kudaden da ba su dace ba. Duk wata tafiya, in dai ba wata fa’ida za ta kawo ga al’umma kasa ba, sai a yi watsi da ita,”in ji shi.