✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin alhazan Kwara 2 sun rasu a Makkah

Rasuwar Alhaji Salman Muhammad Alade da Hajiya Ayishat Shuaib Ologele, ya kai adadin maniyyantan Kwara da suka rasu a Hajjin bana zuwa hudu.

Karin maniyyatan Najeriya biyu daga Jihar Kwara sun rasu a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Rasuwar Alhaji Salman Muhammad Alade da Hajiya Ayishat Shuaib Ologele, ya kai adadin maniyyantan jihar da suka rasu a aikin Hajjin bana zuwa hudu, maza biyu, mata biyu.

HajiyAyishat Shuaib Ologele ta gamu da ajalin ne a hanyar zuwa Makkah daga Madina, a lokacin da ta fadi, amma duk da kokarin da aka yi na ceto rnata ta ce ga garinku nan.

Shi kum Alhaji Salman Muhammad Alade, ya rasu ne daga bisani a birnin Makka.

Kawo yanzu dai babu sanarwa a hukumance game da musabbabin rashe-rashen biyu, amma hukumar jin dadin alhazan jihar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan alhazan.

Babban Sakataren hukumar, Abdulsalam Abdulkadir, ya tabbbatar wa wakiilnmu da rasuwar ta sakon WhatsApp, cewa, “Gaskiya ne mun yi rashin karin maniyyata biyu, za mu yi magana anjima, yanzu ina halartar taro ne.

“Muna mika jajenmu ga iyalansu da kuma rokon samun rahama a gare su”, in ji shi.

Kafin yanzu jihar Kwara ta yi rashin Alhaji Saliu Mohammed da kuma Hawawu Mohammed a kasar Saudiyya.