Fadar Shugaban Kasa ta karyata labarin yi wa Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa da Gwamnoni da wasu masu rike da mukaman siyasa karin albashi da kaso 114 cikin 100.
A ranar Laraba ce dai rahotanni suka ambato wata Kwamishiniyar Hukumar Kula da Rabon Tattalin Arzikin Kasa (RMAFC) na cewa hukumar na shirye-shryen karin albashi ga mutanen.
- Matashiya mai yi wa kasa hidima ta mutu a Gombe
- Bin diddigi: Shin da gaske an bude bodar Legas don shigo da motoci?
Wadanda aka ambato za su amfana da karin albashin dai sun hada da Shugaban Kasa da Mataimakinsa da Gwamnoni da Mataimakansu da Ministoci da Kwamishinoni da mashawartansu da ’yan majalisa da kuma alkalai.
To sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Dele Alake, Shugaban ba shi da masaniya a kan labarin, kuma ba shi da tushe ballantana kamshin gaskiya.
Sanarwar ta ce, “Mun samu labarin da ke yawo cewa an yi karin kashi 114 cikin 100 na albashin Shugaban Kasa, Mataimakin Shugaban Kasa, zababbun masu rike da mukaman siyasa na tarayya da na jihohi da kuma jami’an shari’a.
“Wannan labari ne mara tushe domin babu inda Shugaban Kasa Bola Tinubu ya amince da batun karin albashin, kuma babu inda aka gabatar da wannan kudiri a gabansa domin neman yardarsa.
“Duk da cewa yana cikin kundin tsarin Hukumar Kula da Rabon Tattalin Arzikin Kasa (RMAFC) su ba da shawarar daidaita albashi da alawus-alawus ga masu rike da mukaman siyasa da alkalai, sai dai hakan ba zai iya aiki ba har sai Shugaban Kasa ya yi duba tare da amincewa da shi.
“Sannan kuma hukumar RMAFC, ta hannun Manajan Hulda da Jama’a, ta mayar da martani kan wannan labari na ƙarya da ake yaɗawa, ta kuma bayyana gaskiyar al’amarin,” in ji Dele Alake.
Daga nan sai ya shawarci ’yan jarida da kafafen yada labarai da su guji yada duk labarin da ba su tantane sahihancinsa ba.