✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tilas PDP ta hada kai da APC wajen sauya fasalin Najeriya —Okechukwu

Okechukwu ya ce dole ne PDP ta ajiye adawa, ta zo a yi tafiya tare.

Darakta-Janar na gidan rediyon Muryar Najeriya (VON) Osita Okechukwu, ya bukaci jam’iyyar PDP ta hada kai da APC wajen sauya fasalin Najeriya.

Okechukwu a cikin sanarwar da ya fitar ya ce bai kamata adawa ta siyasa ta shiga lamarin sauya fasalin kasar ba.

“Tun da Gwamnatin Buhari ce ta fito da tsarin sauya fasalin kasa, ya kamata PDP da kowa su shigo a wuce zuwa Kotun Koli don fara sauya fasalin.

“Ina daga cikin masu rajin samun karin jiha daya a Kudu maso Gabas, don ba mu damarmu.

“Ina so mu samu Sanatoci 18, karin ’yan majalisu, karin Kansiloli a yankuna, amma za mu ci gaba da tura kokon bararmu har sai hakarmu ta cimma ruwa,” inji Okechukwu.

Mista Osita ya jima yana bukatar Gwamnatin Tarayya ta sake kirkiro da sabuwar jiha a yankin nasa.

A ranar Asabar ne dai jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci APC ta fito ta yi wa ’yan Najeriya bayani game da matsayarta dangane da sauya fasalin kasar.