Bankin Fidelity ya ce ya shirya tsaf domin karbe ragamar gudanarwar kamfanonin rarraba wutar lantarki na shiyyoyin Kano (KEDCO) da na Kaduna (KAEDCO) da kuma na Benin, sannan ya jinginar da hannayen jarinsu.
Darakta-Janar na hukumar Kula da Kadarori Gwamnati (BPE), Alex Okoh da Shugaban Hukumar Kula da Saha’anin Lantarki (NERC) Sanusi Garba, su ne suka bayyana hakan cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar ranar Laraba a Abuja.
- Idan na zama Shugaban Kasa yajin aikin ASUU zai zama tarihi – Kwankwaso
- Dan kwangilar da ya cinye kudin gyaran gidajen alkalan Kotun Koli ya shiga hannu
Sun ce, “A yau, Bankin Fidelity ya sanar da mu cewa ya kama hanyar jinginar da hannayen jarin kamfanin rarraba lantarkin na Kano da na Benin da kuma na Kaduna.
“Hakan nan, Bankin ya yi yinkurin karbe ragamar gudanarwa na wadannan kamfanoni domin jinginar da hannayen jarinsu.”
Sanarwar ta ce matakin na Bankin Fidelity, abu ne na yarjejeniya da kasuwanci, kuma al’amari ne tsakanin masu zuba jari a kamfanonin da mai ba da bashi.
“An sako hukumar BPE cikin lamarin ne saboda kashi 40 na hannun jarin da gwamnati ke da shi a kamfanonin,’’ inji sanarwar.
Sanarwar ta kuma nuna cewa, yanzu mambobin hukumar gudanarwa da bankin ya nada wa kamfanonin su ne Hasan Tukur na KEDCO, a matsayin Shugaba, sai kuma Nelson Ahaneku da Injiniya Rabiu Suleiman a matsayin mambobi.
A Kaduna kuwa (KAEDCO), Abbas Jega shi ne sabon Shugaba sai kuma Ameenu Abubakar da Marlene Ngoyi a matsayin mambobi.
Sai kuma kamfanin Benin, inda ake da K.C. Akuma a matsayin Shugaba, Adeola Ijose da Charles Onwera su ne a matsayin mambobi.
Yayin da hukumar BPE ta zabi Bashir Gwandu (Kano), Yomi Adeyemi (Benin), da kuma Umar Abdullahi (Kaduna) a matsayin Darakatocin da za su wakilci bangaren gwamnati a kamfanonin da lamarin ya shafa.