✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taurarin Zamani: Dabo Daprof

Ya bayyana cewar nan da shekara 100 Kannywood ba za ta ci gaba ba, idan ba a mayar da hankali kan wasu kurakurai da ake…

Umar Ayuba Isah wanda aka fi sani da ‘Dabo Daprof’ mawakin Hip-hop ne, jarumi kuma malamin makaranta da yake jan zarensa a masana’antar waka ta gambara.

Mawakin a cikin shirin TAURARIN ZAMANI, ya bayyana cewar nan da shekara 100 Kannywood ba za ta ci gaba ba, idan ba a mayar da hankali kan wasu kurakurai da ake tafkawa yayin daukar fim ba.

Sannan ya ce rashin hadin kai a tsakanin mawakan hip-hop na Hausa ’yan uwansa ne ya hana su ci gaba kamar takwarorinsu masu wakar nanaye.