Masana’antun Shirya Fina-finai na Kudancin Najeriya Nollywood da na Hausa Kannywood, sun yi rashin jiga-jigan jarumansu a ’yan kwankin nan.
Da dama daga cikin jaruman da suka riga mu gidan gaskiya sun jima suna jan zarensu a masana’antar.
Daga cikin waɗanda mutuwarsu ta girgiza ’yan Najeriya a Kannywood akwai Darakta Amini S. Bono da Usman Baba Pategi (Samanja) sai kuma ta ƙarshe Saratu Gidado (Daso).
A Nollywood ta Kudancin Najeriya, akwai irin su Tolani Quadri Oyebamiji da ake kira da Sisi Qadr da Ethel Ekpe da kuma Cif Adedeji Aderemi da aka fi sani da Olofa.
A cikin waɗanda suka mutu daga Nollywood akwai John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu da kuma Amaechi Muonagor.
Waɗanda har yanzu ake alhinin mutuwarsu akwai Saratu Gidado (Daso) wadda ta mutu ranar Talata 9 ga watan Afrilu, 2024.
Saratu Gidado (Daso)
Jarumi Usman Baba wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama ya rasu yana da shekara 84 a duniya. Ya bar mata biyu da ‘ya’ya 12.