✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete

Bayan dawowata daga Saudiyya, na fara sha’awar bin sahun iyayena a sana’ar tasu.

Maryam Abubakar, ɗaya ce daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood ’yan ƙalilan da suka yi nasarar bin sahun iyayensu a harkar fim.

Matashiyar jarumar, wadda aka fi sanin ta da Maryam Intete a masana’antar, ta yi bayani a kan matsayinta na wadda iyayenta suka suka a cikin cikin harkar fim.

A wannan tattaunawar, jarumar ta yi bayani game da gogewarta da yadda ake samun daukaka a Kannywood, da wasu abubuwa game da ita kanta da iyayenta, da kuma sana’ar fim da dai sauransu.

Wace ce Maryam Abubakar?

An haife ni ne a Kano kuma a nan na girma. Na yi makarantar firamare da sakandare duk a Kano, daga baya na koma kasar Saudiyya inda na yi shekaru masu yawa a can.

Bayan na dawo Nijeriya ne na shiga harkar wasan fim kamar yadda na riski mahaifiyata na yi.

Ina da shekaru sama da ashirin, dangina na daga cikin masu shirya fina-finai a masana’antar Kannywood.

Idan mutum zai iya cewa sana’ar fim tana gudana a jininsa, to zan iya cewa fim na gudana a jinina, domin mahaifina ya dan yi aiki a masana’antar Kannywood kafin ya daina.

Mahaifiyata kuma har yandu tana ci gaba da taka rawa sosai a harkar shirya fina-finan Hausa.

Wanann ne ya sa na ce wasan kwaikwayo yana gudana a cikin jinina.

Amma duk da haka, ban taba tunani zama ’yar fim ba duk da cewa na kasance wani bangare na rayuwata a cikin harkar ta ginu.

Abin mamaki, bayan dawowata daga Saudiyya, na fara sha’awar bin sahun iyayena a sana’ar tasu.

Ko za ki iya mana karin bayani a kan su waye iyayenki da kika ce suna harkar fim?

Kamar yadda na faɗa a baya, mahaifina ya ɗan yi aiki a masan’antar amma mutane da yawa ba za su iya tunawa da shi ba ko da na ambaci sunansa.

Mahaifiyata kuma ta kasance ginshiki mai karfi a tarihin Kannywood, har yanzu tana taka rawa sosai a masana’antar domin tarihin masana’antar fina-finan Hausa ba zai cika ba sai an ambaci sunanta da kuma rawar da ta taka wajen ci gaban masana’antar.

Ba wata ba ce illa malama Hauwa Garba wadda aka fi sani da ’Yar Auta ko Sabura a cikin shirin Gidan Badamasi.

Ni ’yarta ce kuma ko ku yarda ko kar ku yarda nagartar mahaifiyata ce ta ja ni Kanywood.

Ana girmama ni saboda kasancewarta ’yarta kuma duk sauran ’yan wasan da na hadu da su a masana’antar a shirye suke su ba ni duk wata gudummawa da goyon baya da nake bukata.

Tun yaushe kike masana’antar Kannywood?

Yanzu dai na yi fiye da shekara biyu, kuma abin al’ajabi da sha’awa, shi ne, a cikin wannan ɗan gajeren lokaci, na yi fina-finai da yawa kuma na taka rawa a cikin kusan finafinai hudu.

Haka kuma, masu shirya fina-finai a kodayaushe suna son su saka ni a finafinansu musamman idan sun fahimci cewa ni ’yar Yar Auta ce.

Bayan fina-finan da na fito a ciki, ina da sauran fina-finan da ke jira na.

Dole ne in nuna godiya ta kwarai ga furodusoshin Kannywood bisa yadda suka amince da kuma yarda da iya wasana, dole kuma in yaba wa mahaifiyata saboda ta saukaka min tafiya, ta hanyar zama abin koyi ga yawancin matasa masu basira.

Yaya za ki kwatanta ranarki ta farko a gaban kyamara?

Ko da yake ba bakon abu ba ne a gare ni, amma bai kasance mai sauki kamar yadda nake tsammani zai kasance ba.

Idan za ka iya tunawa na gaya maka cewa na taso ne a cikin dangi inda wasan kwaikwayo ya bunkasa kuma don haka na san duk abubuwan da ke ciki.

Amma ba kamar yadda nake tunani ba, rana ta farko ta tabbatar mini da cewa akwai abubuwa da yawa fiye da abin da muke tsammanin harkar fim ta kunsa.

Abun burgewa shi ne kowa a shirye yake ya taimaka min kuma ya karfafa min gwiwa domin yin nasara.

Mene ne ra’ayin mahaifiyarki yayin da kika so shiga Kannywood?

Maganganun mahaifiyata su suke kara min karfin gwiwa wajen yin gaba kuma ina ganin tasirinsu a cikin tafiyata.

Ta ce da ni, “Maryam dole ne ki girmama kowa a wannan masana’antar, su ne manyanki kuma su ma za su yi miki jagora, ki tuna fa abokan aikin mahaifiyarki ne.”

“Wannan shi ne sirrina, ina mutunta kowa da kowa a masana’antar, kuma duk sun kasance kamar dangi ne a gare ni.

Za ki iya fitowa cikin fim daya tare da mahaifiyarki?

Fitowa a fim ɗaya tare da mahaifiyata abin alfahari ne gare ni, fim shi ne sana’ar da muke yi don dogaro da kanmu, mahaifiyata ta shahara a Kannywood kuma tana da dabi’u masu kyau, da suka cancanci a yi koyi da ita.

Kowa a masana’antar yana girmama ta saboda rawar da take takawa a duk shirin da aka saka ta.

Zan iya cewa fitowata a fim daya tare da ita zai zamo abin alfahari a matsayina na jaruma, dama ce a gare ni wacce ba kowa yake da ita ba.

Babbar nasara ce a gare ni shigowata cikin masana’antar Kannywood tun mahaifiyata tana taka rawar gani a cikinta.

Wanne abu ne ba za ki taɓa mantawa ba a matsayinki na jaruma?

Abin da ba zan taɓa mantawa ba a matsayina na jaruma shi ne duk lokacin da mutane suka nuna sun san ni a matsayin ’yar ’Yar Auta.

Girmamawa da kuma nuna sanayya da suke min a matsayin ’yarta abu ne da nake kauna wanda ba zan taba mantawa da shi ba a rayuwata.

Hakan ya nuna cewa mahaifiyata shahararriya ce, ta yi shuhura sosai a duniya, ta kafa kyakkyawan tarihi da hakan ke bin ’yayanta.

Kina da shirin da kike aikinsa a halin yandu?

Eh, ina aiki a kan shirin talabijin mai dogon zango mai suna ‘Baban Yawa’, kuma kamar yadda na faɗa a baya, ina da wasu ayyuka da ke jira na, amma a yanzu ina aiki a kan shirin mai dogon zango ne kawai.

Shin Maryam tana soyayya?

A gaskiya ba na yin soyayya. Babban abin da na sa a gaba shi ne na yi shuhura a cikin masana’antar, daga baya kuma sauran wasu abubuwa su biyo baya.

Za ki ci gaba da harkar Kannywood bayan kin yi aure?

A’a, ba na tunanin ci gaba, duk lokacin da na yi aure to na bar harkar fim a Kannywood ke nan.

Mece ce shawararki ga masu tasowa a Kannywood?

Su girmama kowa, ba da yawan fina-finai da ka fito ake samun ɗaukaka ba, shahara ita ce yawan mutane da kuka yi hulɗa da su ta hanyar wasan kwaikwayo.