A ranar Talatar Allah Ya yi wa fitacciyar jarumar Kannywood, Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso rasuwa.
’Yan uwan Daso da suka zanta da kafofin watsa labarai sun ce mutuwar fuju’a ce ta riske ta daga kwanciya barci bayan ta yi sahur.
Sai dai wata ’yar uwarta Zeenaru Muhammad Gidado da Aminiya ta zanta da ita ta bayyana cewa, marigayiyar ta yi fama da mura mai ƙarfin gaske har ta kai ga numfashinta yana sarƙewa.
Tuni dai fitattun jarumai irinsu Alhassan Kwalli, Abba El-Mustapha, Baballe Hayatu, Sani Musa Danja da Yakubu Muhammad suka halarci jana’izar Daso.
Aminiya ta ruwaito cewa, an sallaci gawar Daso a Kofar Kudu da ke harabar Masarautar Kano sannan aka binne gawarta a maƙabartar Dan Dolo da ke Goron Dutse.
Tarihin Daso a taƙaice
Rahotanni na cewa an haifi Saratu Gidado a unguwar Gudundi da ke birnin Kano a ranar 17 ga watan Janairun 1968.
Ta kuma soma aikin sakatariya a wani kamfani da kuma koyarwa a wata makarantar Firamare kafin ta soma shirin fim da kamfanin Aneesa Production na Ali Hamisu Indabawa a wani fim mai suna Feleke a ƙarshen shekarun 1990.
Daga baya Kamfanin Sarauniya na Auwalu da Aminu Mohammed Sabo suka bata Daso a fim ɗinsu mai suna Zarge.
A cikin fim ɗin Zarge, Daso ta taka rawar da ta jawo mata shahara da kuma shiga sauran finafinai da dama wanda ta ci gaba duk da ta sake yin aure a farkon shekarun 2000 ta kuma tare a unguwar Sharada da mijinta.
Daso dai ta shahara wajen fitowa a fina-finai na barkwanci da nuna kisisina irin ta ’ya’ya mata.
Daga cikin fina-finan farko da Daso ta fito akwai Linzami da Wuta wanda kamfanin Sarauniya Movies ya shirya a shekarar 2000.
Sauran fina-finan da suka ƙara haska tauraruwar Daso sun haɗa da Nagari, Gidauniya, Mashi da kuma Sansani.
Marigayiyar ta tsunduma harkar tallafa wa mabukata da kuma gajiyayyu daga gidauniyar da ta kafa wacce daga tallafin da take samu daga shirin Aisha Buhari na Feature Assured ta ke rarraba wa birni da ƙauye.
Daso ta shahara da wannan aiki har zuwa lokacin watan Azumin bana lokacin da Allah Ya karɓi ranta.
Ɗaya daga manyan nasarorin da ta samu shi ne shiga cikin sahun jakadun Bankin Musulunci na TAJ a farkon shekarar da ta wuce.
A wata hira da ta yi da Shirin Taurarin Zamani na Aminiya, Daso ta ce ta yi karatun boko har zuwa matakin Diploma da ta samu shaida a Polytechnic ta Kaduna.
Daga nan kuma Daso ta tafi birnin Landan inda ta yi kwas na tsawon wata tara a fannin nazarin halayyar dan Adam wata Human Psychology a Turance.
Ta ce bayan dawowarta ce ta soma koyarwa a wata makarantar Firamare daga nan kuma ta tsunduma a harkar fim.
Bayan sana’ar fim kuma Daso ta shaida wa Shirin Taurarin Zamani cewa tana sayar da turaren wuta wanda take oda daga kasar Chadi.
Ta kuma ce a karkashin gidauniyarta da ke tallafa wa jama’a wadda duk ranar Juma’a tsawon shekaru 15 ana dafa abinci shinkafa fara da mai da yaji ana raba wa almajirai.
A wancan lokacin, Daso ta ce babu abin da zai sa daina sana’ar fim don tana tunanin mutu ka raba ko kuma idan wani dalili na babbar harka ya taso tun daman babu wanda ba ya son ci gaba a rayuwa.
Ɗaya daga cikin masu shirya fim da bayar da umarni da suka sha gwagwarmaya tun tale-tale, Malam Yakubu Liman, ya shaida wa Aminiya cewa, “kusan za a iya cewa ni na fara sa Daso a fim domin ni ne Daraktan Feleke.
“A lokacin da ta je audition a Sarauniya suka ki sanya ta saboda babu wanda ya santa, sai da ta ambaci sunanmu sannan suka ba ta gurbi saboda alakar da ke tsakaninmu da su.
“Ta kuma taba bayyana hakan a wata tsohuwar hirarta da Mujallar Fina-Finai ta Fim Magazine, a cewar Malam Yakubu.