DSP Imam Ahmad Adam Kutubi
Yau cikin yardar Allah za mu fara tsakuro wani abu ne daga littafin Kitabut Tauhid da DSP Imam Ahmad Adam Kutubi ya fassara kuma ya aiko mana muna fata za a karu da abin da littafin yake karantarwa; Bismillah:
Babi na daya
Dalilin halittar mutum da aljan:
Allah Ya ce a cikin Alkur’ani Mai girma, “Ban halicci mutum da aljan ba, sai don su bauta Min. Ba Na bukatar wani arziki daga gare su, kuma ba Na neman su ciyar da Ni. Lallai ne Allah, Shi ne Mai azurtawa kuma Ma’abucin karfi.” (Zariyati, 56-58). A wata aya kuma Allah Yana cewa, “Hakika kowace al’umma Mun aika mata da wani Manzo a kan su bauta wa Allah su nisanci dagutu.” (Nahli, 36). Ma’anar dagutu, duk wani abin da ake bautawa ba Allah ba, kamar Mala’iku ko Annabawa ko aljanu ko waliyai ko salihai da sauransu.
A wata aya kuma Allah Yana cewa, “Hakika Allah Ya yi horo a kan a bauta maSa Shi kadai, kuma a kyautata wa iyaye biyu. Koda dayansu ya tsufa ko dukansu biyu, idan magana ta tashi tsakaninka da su, kada ka ce musu tir, kada kuma ka yi musu tsawa. Ka yi musu magana kyakkyawa ka tausasa musu, kuma ka nuna kai ba komai ba ne a gabansu. Idan kuma za ka yi musu addu’a, sai ka ce, ‘Allah Ka jikan mahaifana kamar yadda suka raine ni tun ina karami har na girma.” (Isra’i, 23). Kuma a wata ayar, sai Allah Ya ce, “Ku bauta wa Allah Shi kadai, kada ku hada Shi da kowa.” (Nisa’i, 36).
Allah Ya sake cewa a cikin LittafinSa: “Ka ce: “Ku zo in karanta muku abubuwan da Ubangijinku Ya haramta.” Wajibi ne a kanku kada ku yi shirkin komai da Shi, su kuwa mahaifa biyu (ku kyautata musu) kyautatawa, kada ku kashe ’ya’yanku saboda talauci, Mu ne Muke azurta ku da su, kuma kada ku abubuwan kusanci alfasha abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya boyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta face da hakki. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da shi: tsammaninku, kuna hankalta. Kada ku kusanci dukiyar maraya face da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga karfinsa. Kuma ku cika mudu da sikeli da adalci, ba Mu dora wa rai wani nauyi face iyawarsa. Kuma idan kun fadi, to ku yi adalci, kuma koda ya kasance ma’abucin zumunta ne. Kuma ga alkawarin Allah ku cika. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi, tsammaninku, kuna tunawa. Kuma lallai wannan shi ne tafarkiNa madaidaici: sai ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi su rarraba da ku daga barin hanyaTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi, tsammaninku kuna yin takawa.”
(An’am: 151-153).
An ruwaito cewa Annabi (SAW) ya zana layuyyuka a gefen dama sannan ya yi a gefen hagu. Sai ya yi wani dogon layi a tsakiya ya nuna shi ya ce: “Wannan shi ne tafarki madaidaici ku bi shi (wato Alkur’ani da Hadisi). Amma kada ku bi wadancan hanyoyi sai su kai ku ga halaka.
Har yanzu dai an ruwaito daga Ibn Mas’ud ya ce, “Wanda yake son ya ga wasiyyar Annabi Muhammad (SAW) wacce take da ita ce ya cika, to ya karanta ayar da Allah Yake cewa: “Ka ce: “Ku zo in karanta muku abubuwan da Ubangijinku Ya haramta.” Wajibi ne a kanku kada ku yi shirkin komai da Shi…” har zuwa inda Allah Yake cewa, wannan shi ne tafarkiNa madaidaici: sai ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi su rarraba da ku daga barin hanyaTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi, tsammaninku kuna yin takawa.”
(An’am: 151-153).
An samu wani Hadisi daga Mu’azu dan Jabal (RA) ya ce: “Wata rana muna tare da Annabi (SAW) a kan jaki sai ya ce, “Mu’azu ka san hakkin Allah a kan bayi kuwa, kuma ka san hakkin bayi a kan Allah?” Sai Mu’azu ya ce, “Allah da ManzonSa ne kawai suka sani.” Sai Annabi ya ce, “To bari in fada maka, hakkin Allah a kan bayi. Su bauta Masa Shi kadai kada su yi tarayya da Shi da kowa. Amma hakkin bayi a wajen Allah shi ne Allah Ya yi alkawarin ba zai kona wanda bai yi tarayya da Shi da kowa ba.” Sai Mu’azu ya ce da Annabi: “Ya Manzon Allah, ko in yi wa mutane bushara da wannan?” Sai Annabi ya ce masa, “A’a kada ka yi domin kada mutane su ki aiki su dogara da wannan.” (Buhari da Muslim suka ruwaito).
Babi na Biyu
Falalar Tauhidi da abin da yake kankare zunubi:
Allah Ya ce, “Wadanda suka yi imani da Allah ba su hada imaninsu da zalunci ba, to wadannan suna cikin aminci kuma su ne shiryayyu.” (An’am, 32). Wani Sahabi da ake kira Ubadata dan Samit (RA) ya ce, “Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ya yarda da babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Shi kazai Yake ba Ya da abokin tarayya kuma Annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma ManzonSa ne, kuma ya yarda Annabi Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne, kuma kalma ce da aka jefa cikin Maryam (ma’anar kalma ita ce, “KUN FA YAKUN,” kuma shi Annabi Isah rai ne daga wajenSa (ma’anar rai shi ne rai ne daga rayukan da Allah Yake sanya wa bayi), sa’annan mutumin ya yarda da cewa Aljanna gaskiya ce kuma wuta gaskiya ce, to Allah Ya dauki alkawarin zai sanya shi a Aljanna gwargwadon aikinsa.”
(Buhari da Muslim suka ruwaito).
Itban (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Duk wanda ya ce: ‘La’ilaha illal-lahu’ bai kuma warware ta ba, ya kuma nemi yardar Allah da ita, to Allah Ya haramta wuta ta kone shi.” Abu Sa’idul Khudri (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya ba da labarin cewa Annabi Musa (AS) wata rana ya ce: “Ya Ubangiji! Ni ina so Ka ba ni wata addu’a ta musamman wacce zan rika kiranKa da ita ina rokonKa da ita.” Sai Allah Ya ce, “Eh,” haka ne amma, ita ‘La’ilaha illal-lahu’ da za a dauki sammai bakwai da duk abin da ke cikinsu ban da Ni da kuma kassai bakwai a sanya a sikeli, sannan a dauki ‘La’ilaha illal-lahu’ a sanya a dayan gefen sikelin, sai ta rinjaye su duka.” (Ibn Hibban da Hakim suka ruwaito kuma sun ce Hadisi ne ingantacce).
Imam Tirmizi ya ce: “Ya ji daga Anas cewa Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Allah Ya ce a Hadisin Kudusi, “’Ya kai dan Adam! Da za ka zo Min da laifi mai yawa misalin yawan kasa, ka hadu kuma da Ni ba ka yi shirka ba, to da sai in zo maka da kwatankwacinsa na gafara.”
DSP Imam Ahmad Adam Kutubi
Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3,
Abuja, 08036095723