✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka cikin shekaru uku masu zuwa — Bankin Duniya

Bankin Duniya ya yi kira da a ba da fifiko ga sauye-sauyen tsarin da ke inganta ci gaban kamfanoni masu zaman kansu.

Bankin Duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka ba tare da taɓarɓarewa nan da shekaru uku masu zuwa.

Bankin ya yi hasashen haɓakar ma’aunin tattalin arzikin cikin gida, GDP da kashi 3.6 cikin 100 a shekarar 2025, sai kashi 3.7 a shekarar 2026 da kuma kashi 3.8 a shekarar 2027.

A cewar sabon rahoton tattalin arzikin duniya da Bankin ya fitar, ana sa ran za a tallafa wa matsakaicin lokaci na Nijeriya ta hanyar samar da ingantattun albarkatun mai, da gyare-gyaren da ake ci gaba da yi, da kuma farfado da ƙwarin gwiwar masu zuba jari.

Rahoton ya yi nuni da cewa, yayin da tattalin arzikin kasar ke shirin fadada, kalubale irin su hauhawar farashin kayayyaki, da matsalar canjin kudi, da kuma gibin kasafin kudi na ci gaba da zama babbar barazana ga ci gaba mai ɗorewa.

Bankin ya kuma kara da cewa, aiwatar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki da gwamnatin Nijeriya ke yi, musamman ta fuskar farashin makamashi da tattara kuɗaɗen shiga, da sarrafa kuɗaɗen musaya, zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da waɗannan hasashen ci gaban.

Ana sa ran ci gaban Nijeriya a shekarar 2025 zai kasance matsakaici da kashi 3.3 cikin 100, yayin da matsalolin tsarin ke ci gaba da yin la’akari da saurin farfadowar tattalin arziki.

Bankin Duniya ya yi kira ga masu tsara manufofin Nijeriya da su ba da fifiko ga sauye-sauyen tsarin da ke inganta ci gaban kamfanoni masu zaman kansu, inganta ababen more rayuwa, da inganta jarin ɗan Adam don ɗorewar bunkasar tattalin arziki na dogon lokaci.