Masu ruwa-da-tsaki a Najeriya sun gargadi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu cewa matukar ya ki bin shawararin da Hukumar Bayar da Shawara kan Tsare-Tsare da Dokoki ta Kasa ta ba shi ta bi sannu a hankali, to ’yan Najeriya da dama za su afka cikin kangin talauci.
Masu ruwa-da-tsakin sun ce duk da yawancin tsare-tsarensa na farfado da tattalin arziki suna da kyau amma kada ya rika gaggawa ta yadda a karshe za a yi wa Najeriya sakiyar da ba ruwa.
- Malamar jinya ta yi ta bakin aikinta bayan lalata da marar lafiya a Birtaniya
- Cutar Diphtheria ta kashe mutum 80 a Najeriya — NCDC
Sun ce ya kamata Shugaban ya fito tallafin da zai rage wa miliyoyin ’yan Najeriya tsananin da suke fama da shi.
Za a iya samun karuwar matalauta miliyan 7 — Bankin Duniya
Bayanin nasu na zuwa ne jim kadan bayan bayyana illar da cire tallafin man fetur ya haifar da Bankin Duniya ya fitar cewa har ya talauta ’yan Najeriya sama da mutum miliyan hudu.
Masanin Tattalin Arziki kuma wakilin Bankin Duniya a Najeriya, Alex Sienaert ne ya bayyana haka yayin kaddamar da rahoton ‘Halin da ake ciki kan ci gaban Najeriya’ a Abuja.
Sienaert ya yi gargadin cewa matukar ba a dauki wasu kwararan matakai tare da zartar da su ba, za a samu karin ’yan Najeriya miliyan 7.1 da za su sake afkawa cikin talauci zuwa nan da karshen shekara.
Yayin da yake bayani kan sauya fasalin tattalin arzikin kasar, wani masanin tattalin arziki, Farfesa Uche Uwaleke ya ce babu shakka Shugaba Tinubu ya kama hanyar kai Najeriya tudun-mun-tsira domin yana yin abin da ya dace.
“Amma duk da haka, ya kamata a rika aiwatar da sauyin mataki-mataki kuma cikin tsanaki.
“Idan har Shugaban yana bin kudirori da shawarwarin da kwamitin Sanata Tokunbo Abiru ke jagoranta wanda ya tsara cewa a cikin kwana 100 na mulkinsa ne Shugaban zai bayyana aniyarsa ta cire tallafin man fetur sannan daga baya kamar yadda aka tsara a takardar zai gabatar da shirin tallafa wa ’yan Najeriya don saukaka musu radadin kuncin da za su shiga sanadiyyar wannan shiri.
Sannan sai batun albashi mafi kankanta da kuma hada kai da Dangote da BUA don kara adadin abin da suke sarrafawa don amfanin jama’a.
Farfesa Uwaleke ya ce a bangaren tsarin lamuni kuma an bayar da shawara cikin kundin kwamitin cewa akwai bukatar da farko a samar da wata shimfida da za ta haifar da tasiri wajen musayar kudade bai-daya ga tsarin tattalin arzikinmu daga nan sai a gane nawa ne za a bukata kuma daga asusun ajiya da ke waje don tallafa wa shirin.
“Wadannan abubuwa ya kamata a fara lura da su kafin a fara batun daidaita farashin bai-daya a musayar kudi, amma kwatsam sai muka ga an fara aiwatar da wasu abubuwa tun kafin fara amfani da shawarwarin da aka mika,” in ji shi.
Idan za a iya tunawa, Kwamitin Masana Tattalin Arziki na Kamfanin Daily Trust ya fitar da takardar bayan taro a makon jiya inda a ciki ya bayyana cewa gaggawar aiwatar da manufofi da tsare-tsaren Shugaba Tinubu za ta jefa ’yan Najeriya a cikin talauci ta fuskoki daban-daban matukar aka ci gaba da tsarin ’yanta tattalin arzikin ba tare da samar da mafita ta hanyar bin matakan sassauta wa ’yan kasa ba.
Cikin takardar bayan taro da Shugaban Kwamitin, Farfesa Binta Tijjani Jibril ta sanya wa hannu, mambobin Kwamitin Tattalin Arzikin sun yaba wa tsare-tsaren Shugaba Tinubu kan sauyesauyen da yake kawowa domin daidaitawa da saita tattalin arzikin kasa kan hanya mai dorewa.
Sai dai kwamitin ya nusar da Shugaban cewa takaitaccen tasirin shirin zai aike da ’yan Najeriya da suka iya jure wa rashin iya tafiyar da tattalin arziki daga gwamnatin da ta gabata mummunan sako zuwa a kwalkwalensu.
Kwamitin ya ankarar kan yadda aiwatar da ireiren wadannan tsare-tsare suka tilasta wasu jihohi rage ranakun aiki ga ma’aikata wanda hakan na da nasa hadarin da zai shafi tattalim arziki da zama barazana ga masu gudanar da kananan da matsakaitan sana’o’i a wuraren da ma’aikatan ke ayyukansu.
Mafita Kamar yadda kwararru suka fada, Bankin Duniya ya mayar da hankali ne kan irin hanyoyin fanshe wahalhalun da ’yan kasa marasa galihu za su shiga na takura a sanadiyyar wannan tsari domin kare iyalai daga shiga cikin dimuwa sakamakon hanyoyin gyaran da aka dauko na sauya fasalin tattalin arzikin ta hanyar cire tallafin mai.
Bankin Duniya ya bayyana cire tallafin da aiwatar da musayar kudaden waje a matsayin hanyoyin sauye-sauye da ke bukatar bin mataki sannu-sannu don tunkarar matsalar rashin daidaito a lamarin.
Kwamitin ya ce wannan gagarumin aiki na bukatar dora shi bisa tubali mai kyau da karko.
A cikin wani rahoto, bankin ya kuma bayyana irin sakamakon da hakan zai haifar da ya hada da hauhawar farashin kaya da basussuka da kusan kashi 46.
Sai dai duk da haka ya yarda cewa matakan kawo sauyin da cire tallafin sun dace wajen farfadowa da kuma sake gina tafarki mai dorewa na tattalin arziki.
Bankin Duniya ya yi hasashen tattalin arzikin Najeriya zai karu da kashi 3.3 a bana sannan zuwa badi (2024) zai karu da kashi 3.7 yayin da a shekarar 2025 zai kai zuwa kashi 4.1.
A tattaunawa da masruwa-da-tsaki sun bayyana hanyoyi da dama da za a bi don haifar da sauye-sauyen tattalin arziki tare da kauce wa shiga wahala musamman da marasa galihu ka iya shiga.
Gwamnan Jihar Abiya, Mista Alex Otto da takwaransa na Jihar Oyo, Seyi Makinde sun bayyana bukatar yunkuri na bai-daya don sassauta wa talakawa.
Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Chaudhuri Shubham ya bayar da shawarar tsarin tura wa ’yan Najeriya kyautar kudade a asusun ajiyarsu na banki don saurin shawo kan matsalolin iyali.
Shi ma Farfesa Uwaleke ya ce bai kamata a tilasta wannan tsari ba saboda irin aubuwan da yin hakan zai haifar.
“A cikin kundin shawarwarin an ce gwamnati na burin samun karin kudaden shiga ne da kashi 7 a takaice nan da shekara takwas.
“Sannan ana so a cire mutum miliyan 100 daga talauci tare da samar da ayyuka miliyan 60, ke nan idan aka ce za a yi wannan sauyin nan take to akwai yiwuwar cutar da mutane a kai.
Ya ce, “Za ka iya samun inda kudin shiga na yin kasa yayin da farashi kuma na hauhawa.
“Idan samun kudin shiga ya yi kasa ta yaya za a iya fitar da mutane daga talauci? Maimakon haka ma sai dai a samu tsarin da zai sake tunkuda su cikin talaucin.”
Ya ce tunda har an riga an shelanta cire tallafin, hanya daya kawai da gwamnati za ta iya bi shi ne ta gaggauta yin duk wani sassauci tare da karin albashi mafi karanci mai gwabi.
“Sai dai mafi muhimmanci shi ne duk wani dauki da gwamnati za ta bayar kada ya kasance na madarar kudi. Kada a yi amfani da rabon madarar kudi na Dala miliyan 800 na rancen Bankin Duniya.
“Akwai sassa hudu na talauci da suka hada da fannin ilimi da na kiwon lafiya da na rayuwa yadda ya kamata. Su yi kokari su sa su a fannin kiwon lafiya musamman.
Kwamitin Tattalin Arziki na Daily Trust ya shawarci gwamnati ta gaggauta fahimtar da ’yan kasa su gane abin da ake magana kan cire tallafin man fetur da tsarin bayar da bashin yin karatu ga dalibai da tsarin musayar kudin kasashen waje da kuma dalilin yunkurin karin kudin wutar lantarki da take shirin yi don makomar tattalin arzikin kasar nan.