✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tashin bam a mashaya ya hallaka mutum 7 a Taraba

Ana fargabar mutane da dama sun samu raunuka, ciki har da mata da kananan yara

Ana fargabar mutane da dama sun mutu bayan wani bam da aka dasa a wata mashayar giya ya tashi a garin Iware da ke Karamar Hukumar Ardo Kola a Jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na yammacin Talata.

Aminiya ta gano cewa bam din ya fashe ne a mashayar da ke makare da mutane.

Ana zargin wani mutum ne ya jefa bam din a mashayan inda ya tashi nan take ya halaka mutane bakwai wasu mutane 19 kuma suka sami raunuka.

Wanda ake zargin ya jefa bam din ya shiga hannu, inda nan take aka kama shi aka kuma kashe shi.

Sama da mutum 20, ciki har da mata da kananan yara ne suka samu raunuka, kuma tuni aka garzaya da su Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Jalingo.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin

Sai dai ya ce sun tabbatar da mutuwar mutum uku ne, wasu 19 kuma da suka samu raunuka suna asibiti.