Tsakanin 26 zuwa 29, ga watan Oktoban da ya gabata Cibiyar Wakafi ta Kasa da hadin gwiwar Sashen Koyar da Shari’ar Musulunci da Cibiyar Fahimtar Addinai da Tattaunawa, dukansu na Jami’ar Bayero da ke Kano suka gudanar da taron duniya karo na biyu a kan Wakafi a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano. Taron mai taken “Inganta Cibiyoyin Wakafi a Duniya: Ci gaba da Kalubale,” Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II wanda ya samu wakilcin Mai girma Hakimin Rimin Gado, Sarkin Shanun Kano, Alhaji Shehu Mohammed Dankadai ne ya bude shi.
Masana ilimin Fikhu da na shari’a na ciki da wajen kasar nan ne suka gabatar da kasidu daban-daban, irin su Imam Abdullahi Ehimaeze Emetumah III, kuma Basaraken masarautar Umuofor da Farfesa F R A Adeleke, Shugaban Sashen Shari’a na Jami’ar Jihar Legas da Zeinol Abedien Caje, Shugaban Cibiyar Wakafi ta Afirka ta Kudu da Dokta Ibrahim Nuruddeen na Gidauniyar Wakafi ta Sadiyya da ke Kano da Mukaddashin Daraktan Cibiyar Fahimtar Addinai da Tattaunawa ta Jami’ar Bayero da ke Kano.
Kamar yadda malamai sukan karantar da mu, Wakafi na daga cikin ayyukan ibada da ake fata al’ummar Musulmi su rika yi wajen jibintar rayuwar marasa hali, bayan ayyukan kyautata rayuwar al’umma na yau da kullum da suka saba aiwatarwa don neman lada daga Allah, irin su fitar da Zakka da sadaka da sauransu. Akan yi Wakafi a kan gida ko gona ko dakin karatu ko makaranta da sauransu.
Alal misali akan yi Wakafi a kan gida ko gona wajen samun kudaden hayarsa ko sayar da amfanin gonar da aka noma, sannan a juya kudaden wajen taimaka wa bayin Allah mabukata. Haka mutum na iya cika dakin karatu da littafai iri-iri da sauran bukatu na dakin karatu, don amfanin al’umma. A takaice duk abin da aka yi Wakafi da shi, ya tashi daga mallakar mai shi ko magadansa, don kuwa kayan Wakafi na al’umma ne, don haka magada, ba sa gadonsa, haka su ma al’ummar, wato dai kadara ce ta dindindin don moriyar al’umma.
Wasu daga cikin batutuwan da taron na duniya na Wakafi da aka gudanar a Kano ya yi la’akari da su, kamar yadda sanarwar bayan taron da Shugaba da Sakataren Taron suka rattaba wa hannu, wato Dokta Mohammed Tajudeen Sadik da Dokta Ibrahim Nuraddeen, ta bayyana, sun hada da irin muhimmiyar gudunmawar da Wakafi yake bayarwa ga bunkasa rayuwar al’umma, kamar raba arziki da samar da ayyukan yi. Sun yi la’akari da cewa a ’yan shekarun nan ana ta kara samun fahimtar bukatar a kafa cibiyoyin Wakafi a tsakanin al’ummar Musulmi masu hali a kasar nan, amma hakan bai kai yadda ake bukata ba. Kazalika mahalarta taron sun nanata bukatar da ake da ita ta a rika kakkafa cibiyoyin Wakafi don tallafa wa mabukata.
Sun kuma yi la’akari da cewa a kasar nan babu cibiyoyin Wakafi da za su rika taimaka wa dalibai, musamman a manyan makarantun kasar nan. Ya kuma zama wajibi inji su, al’adar ba da Wakafi da yada ta tare da fadada ta a tsakannin al’ummar Musulmin kasar nan, kwatankwacin abin da ke faruwa a tsakanin al’ummar Musulmin Afirka ta Kudu. Taron ya duba rashin amana da kuma rashin iya tafiyar da kudaden tallafa wa al`’mma. Sun kuma ce wasu manyan makarantu da cibiyoyi na duniya an kafa su ne da asusun Wakafi.
Kamar kowane taro, bayan la’akari da matsaloli da kalubale a kan abubuwan da ake so a cimmawa da yakan ba da shawarwari kan yadda za a shawo kan matsaloli da kalubalen da aka gano, shi ma taron na Kano a kan Wakafi bai yi kasa a gwiwa ba a kan haka. Kamar yadda sanarwar bayan taron ta bayyana wasu daga cikinsu kamar haka:Musulmi ’yan boko, lallai su yi amfani da dukan damar da suka ci karo da ita musamman ta gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan da sauran dokoki don samar da cikakkiyar damar tabbatuwar Wakafi a dokance a kasar nan. Su ma malama magada Annabawa, taron ya shawarce su kan su tashi tsaye wajen yada muhimmacin da ke akwai wajen kafa cibiyoyin Wakafi a kasar nan. Kuma taron ya nemi kafofin watsa labarai su ba da tasu gudunmawar don samun nasarar aikin da aka sa a gaba.
Hakazalika, sanarwar ta nemi al’ummar Musulmi su zauna cikin shirin ba da gudunmawa komai kankantarta ga cibiyoyin Wakafi, ta yadda tallafin zai zamo na kowa da kowa, ba sai masu kudi kadai ba, kamar yadda Musulmin Afirka ta Kudu suka yi wajen tallafa wa asusun cibiyoyin Wakafi na kasar. Samuwar hakan in ji sanarwar, za ta sa ayyukan cibiyoyin su bunkasa, har su iya sauke nauyin mabukatan da ya kamata a taimaka mawa. A shawarar mahalarta taron, manyan makarantun kasar nan su rika kafa cibiyoyin Wakafi da za su rika tallafa wa dalibansu da suke son cimma burinsu na karatu, amma rashi na kawo musu koma baya.
Don samun nasarar kafuwar cibiyoyin Wakafi a manyan makarantun kasar nan mahalarta taron sun ce ya kamata Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), ta sanya a cikin sharuddan bayar da izinin amincewa da karatun kowace jami’a, cewa lallai sai jami’ar ta kafa wata gidauniya a jami’ar. Su ma sauran hukumomin da suke kula da manyan makarantu ya kamata su gindaya wannan sharadi. Hikimar haka bai wuce yadda za a rika barin dalibai mabukata da sukan kasa cimma burinsu na yin karatun da suke so, don kawai ba su da hali su samu hakan ba. Su ma iyayen al’umma sarakuna, fatar taron ne su rika shigewa gaba a masarautunsu, wajen ganin ana kafa cibiyoyin Wakafi kuma suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ko shakka babu, yadda kullum a kasar nan masu shi suke dada more rayuwarsu, saboda abin da suka mallaka na dukiya, yayin da talakawa suke kasancewa kullum a cikin kuncin rayuwa abin a duba ne.
Hatta Zakkah da Allah Ya farlanta wa masu hali su fitar su bayar da ita ga mabukata, yanzu an kai fagen da ba kowane mai hali ke iya fitar da ita yadda Allah Ya yi umurni ba, balle yadda ya kamata ya rabat a ga al’ummar da Allah Ya ambata. Da irin wannan hali ke nan mai karatu ka ga tilas mabukatan kasar nan su sha wahala. Kada ka yi batun sauran ayyukan tallafa wa al’umma da akasarinsu suka koma na riya a wannan zamani.
Da wannan ke nan samun jama’a masu kamanta gaskiya da rikon amana da kuma shigewa gaba na mahukunta (na kowane bangare), za a iya hada karfi da karfe a wannan lokaci a dukufa wajen kafa cibiyoyin Wakafi a kowane lungu da sako na kasar nan. Yanzu kuma shi ne lokacin, don haka sai in ce Allah ida nufi.