A wasan jiya Lahada tsakanin kulob din Brescia da Cagliari, tsohon dan wasan Inter Milan da Manchester City, Mario Balotelli ne ya dauki hankali, inda ya karbi jan kati minti 7 kacal bayan shigowarsa filin wasa.
Shi dai Balotelli, tsohon dan wasa ne da duk duniyar kwallo ta san kwarewarsa wajen taka leda, sai dai zargin rashin da’a ne ka dawo da lamarinsa baya.
Yana cikin ’yan wasan da suke lashe kufuna uku ciki har da ta Zakarun Turai a Inter Milan a shekarar 2010 baya ga Gasar SeriE A guda 3 da ya lashe, sannan ya lashe Gasar Firimiyar Ingila guda 1 da Manchester City da sauransu da ya lashe ko dai a matsayin kulob, ko kuma na kan shi, amma sai dai a duk inda ya je, rikici da jawo cece-kuce kan danne kokarinsa.
A wasan jiya, Balotelli ya shigo wasan ne daga baya, amma cikin mintu 7 kacan ya samu katin gargadi guda biyu, wanda hakan ya sa ya samu jan kati.