✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifin tsohon Gwamnan Kaduna ya rasu

An yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 8:30 na daren yau bayan sallar Isha’i a Unguwar Ƙaura da ke cikin birnin Zariya.

Mahaifin tsohon Gwamnan Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda Masarautar Zazzau ta tabbatar.

Alhaji Ramalan Yero, wanda ɗaya ne daga cikin dattawa kuma mai riƙe rawanin Turakin Dawakin Zazzau ya rasu ne da yammacin wannan Litinin ɗin bayan fama da doguwar jinya.

Marigayi Alhaji Ramalan Yero mahaifi ne ga tsohon Gwamnan Kaduna kuma Dallatun Zazzau, Dokta Muktar Ramalan Yero.

Wata sanarwa da Sarkin Fadar Zazzau, Alhaji Abbas Ahmed Fatika, ya fitar ta ce an yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 8:30 na daren yau bayan sallar Isha’i a Unguwar Ƙaura da ke cikin birnin Zariya.