Masarautar Zazzau ta sanar da soke Hawan Bariki a wannan sallar ta bana — ɗaya daga cikin haye-hayen shagulgulan Sallah na al’ada da masarautar ke gudanarwa a washegarin idin ƙaramar Sallah.
A bisa al’adar Hawan Bariki, Sarkin Zazzau ya kan kai wa Gwamna gaisuwar sallah tare da duk hakimansa yayin da mazauna za su yi dakon wadanda ke haye-hayen dawakan a gefen titi su ma suna yi wa Sarki gaisuwar ban girma.
- Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana
Sarki yakan jagoranci tawagar masarautar ta Zazzau inda zai ratsa ta cikin garin Zazzau sannan ya shiga unguwar Sabon Gari inda zai ziyarci Gwamna a gidan da aka tanada tun zamanin turawan mulkin mallaka.
Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun Masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar, ya ce an soke hawan sakamakon dalilai na aikin gyaran titi da shimfida sabuwar kwalta da ake yi a kan hanyar Kofar Doka zuwa kwanar Agoro.
Ya ce wannan aikin hanya da ake kan yi zai kawo cikas ga masu haye-hayen dawakai da kuma al’umma baki daya.
“Saboda haka wannan shi ne dalilin da Masarautar Zazzau ta soke Hawan Barikin da ake gudanar a washegarin Sallah karama” a cewar sanarwar.