✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarihi, asali da kuma bunkasar adabin wasan kwaikwayon Hausa

Sunan Littafi: Rubutaccen Wasan Kwaikwayo A Rukunin Adabin Hausa: Habakarsa da MuhimmancinsaSunan Marubuciya: Dakta Sun diaomengShekarar  Wallafa:    2013Kamfanin Wallafa:  Gidan Dabino Publishers,     KanoYawan Shafuka:…

Sunan Littafi: Rubutaccen Wasan Kwaikwayo A Rukunin Adabin Hausa: Habakarsa da Muhimmancinsa
Sunan Marubuciya: Dakta Sun diaomeng
Shekarar  Wallafa:    2013
Kamfanin Wallafa:  Gidan Dabino Publishers,     Kano
Yawan Shafuka: 356
Mai Sharhi: Khalid Imam

Dakta Sun diaomeng mace mai kamar maza, ’yar kasar Sin a littafin da ta rubuta mai taken Rubutaccen Wasan Kwaikwayo A Rukunin Adabin Hausa: Habakarsa da Muhimmancinsa  (2013) ta yi waiwaye adon tafiya don binciko da kuma bayyana wa masu karatu cikakke kuma ingantaccen tarihin samuwar adabin wasan kwaikwayon Hausa. Malamar Hausar, sha’awarta a fagen nazari da bincike kan harshen Hausa ko adabin Hausa ta kara fitowa fili, sakamakon wannan littafi da ya kawo bayanai daga bakin masana game da ire-iren wasannin kwakwayo da kuma dalilan da suka haifar da bunkasar wasan kwaikwayon Hausa. Babu shakka ta cancanci jinjinar ban girma saboda wannan kokari nata ya kara tabbatar da gaskiyar maganar nan da masana ke yi cewa, harshen Hausa tauraro ne mai hasken gaske wanda haskensa ya game duniyar ilimi tun daga gida kasar Hausa har zuwa kasar Sin da sauran nahiyoyin duniya.
Abin lura da kyau a nan shi ne, marubuciyar ta cancanci yabo ba wai kawai don kasancewarta mutuniyar kasar Sin ta farko wadda ta rubuta kundi mai shafuka har 356 a cikin harshen Hausa ba, sai don mahimmancin littafin wajen cike gibin da ake da shi a wannan bangaren adabi na rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa.
Duk wanda ya nazarci wannan littafi zai lura da irin ingancin salon marubuciyar da kuma kyawun daidaitacciyar Hausar da ta yi amfani da ita a littafin. Babu shakka sauki da kuma irin armashin harshen da ta yi amfani da su manyan hobbasa ne, musamman idan aka yi la’akari da cewa Hausa ba harshen da aka haife ta da shi ba ne. Hakan babbar nasara ce kuma nasarar na iya kawar da dukkan wani kokwanto da mai karatu yake da shi cewar Hausa ba harshe ba ne na duk mutanen duniya. Kamar yadda ta kara tabbatarwa da wannan mahimmin aiki nata cikin harshen Hausa, cewa shi harshe ne mai sauki da dadin sarrafawa wajen yada ilimi da gudanar da bincike ga ma wadanda ba Hausawa ba kuma a ko‘ina suke a fadin duniyar nan.
Babban malamin Hausa kuma Baturen Birtaniya, Farfesa Graham Furniss na Tsangayar Nazarin Al’adu Da Harsunan Afirika da ke Jami’ar Landan ya tabbatar a cikin gabatarwar wannann littafi cewa, adabin wasan kwaikwayon Hausa bai sami kyakkyawar kulawa ko gatan da ya kamace shi ba; musamman idan aka kwatanta wannan fagen da na sauran nau’o’in adabin gargajiya ko zamani. Gatan da adabin wakar baka ko rubutacciyar waka ko kuma rubutun zube suka samu ko kusa adabin wasan kwaikwayo bai samu ba. Idan aka yi la’akari da wannan bayani na Furnis (2013), za a iya cewa adabin wasan kwaikwayo tamkar maraya ne. Duk da wannan maraici da adabin wasan kwaikwayo ke fama da shi wani, muhimmin fage ne na adabi musamman wajen samar da nishadi ko ilimantar da jama’a.
Marubuciyar ta yi kokari sosai wajen bin sahun gwarazan masana kamar irin su marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya wajen zama zakaran gwajin dafi a fagen bincike da nazarin adabin wasan kwaikwayon Hausa. A wannan  littafi marubuciyar ta yi kokari da kuma bin kwakkwafin bayanai, duk don ta gano sahihi kuma karbabben bayani da ya tabbatar da asalin wasan kwaikwayon Hausa. Manazarciyar ta yi dogaro da hujjoji daga bakin masana masu yawan gaske.
Misali, binciken nata ya tabbatar da cewa an dade da samun wasan kwaikwayo rubutacce na Hausa. Kazalika ta ci gaba da tabbatar da cewa idan aka duba kundin digiri na biyu na Adamu Ibrahim Malumfashi mai suna Asali Da Bunkasar Rubutaccen Wasan Kwaikwayo Na Hausa, za a lura cewa ya kawo littattafai 17 da aka yi na wasan kwaikwayo. Kamar yadda ta ruwaito, Malumfashi ya ce littafin Sid Hausa Plays shi ne wasan kwaikwayo na farko a kasar Hausa. Amma kuma a wata kasida da shi malamin ya sake gabatarwa a wani taron kara wa juna ilimi da aka yi a Jami’ar Usman danfodiyo a 1990, mai suna Rubutaccen Wasan Kwaikwayon Hausa Daga Shekarar 1930 zuwa 1990 Sharhi A Kan Matsayinsa, Malumfashi ya nuna cewa “A tawa fahimtar dai tun a shekarar 1902 aka rubuta wani wasan kwaikwayon Hausa” na farko.
Ta ci gaba da  cewa: “Bincike ya nuna cewa wannan wasa da Malumfashi ke magana a kai, daya ne daga cikin wasannin kwaikwayon da Rudolf Prietze da Ahmadu Kano suka yi. Sunan wasan Turbar Tarabulus. Daga baya Ahmed, U.B. ya buga sauran wasannin da wannan Bajamushe ya rubuta da taimakon falke Ahmadu Kano. Sauran wasannin su ne: Tarihin Rabeh (1902) da ’Yan Matan Gaya (1900) da kuma Turbar kudus (1898).”
Ashe ke nan littafin nan abu ne da mai nazari zai iya yin tinkaho da shi wajen kafa hujja a fagen ilimi, musamman idan aka yi la’akari da tarin hujjuji da kuma salo mai armashi da marubuciyar ta gina littafin da su. Saboda samar da saukin karatu da nazari, an rarraba littafin a takaice zuwa manyan kashe-kashe guda biyu. Kashi na farko na kunshe da bayanai ne na sharar fage da suka kunshi irin su: Sadaukarwa da godiya da gabatarwa da ta’aliki da kuma bayani game da ayyukan da suka gabata da wadanda suka shafi bayanai kan asalin wasan kwaikwayo da sauransu.
A kashi na biyu, marubuciyar ta yi sukuwa da zamiya wajen rairayo bayanai, wadanda ta yi wukar gindi da su wajen kafa hujjojinta, wadanda ta gabatar cikin natsuwa da kwarewa, duk ba don komai ba sai don ta tabbatar da cewa duk bayanan gamsassu ne kuma ingantattu. Haka kuma ta rarraba wannan kashi zuwa babi-babi takwas.
Babi na daya wanda a shi ne shimfida, a cikinsa ne ta yi sharar gona ta yin amfani da hujjoji kafin ta zo ga yin shuka a sauran shafukan da ke tafe na littafin. Gabatarwar da ta fara daga shafi 15 ta kuma kare a shafi na 25, na kunshe da bayanai kan ma’anar adabi da rabe-raben adabin Hausa da nau’o’insa, wato su: waka da zube da wasan kwaikwayo.
A babi na biyu wanda ya fara daga shafi na 27 zuwa 64, mai karatu zai yi tozali da gamsassun bayanai a kan tarihin rubutu a kasar Hausa. Kazalika a wannan babi malamar ba ta yi tuya ta manta da albasa ba, domin kuwa ta bi diddigin kyakkyawar gudunmowar da wasu mashahuran malaman Musulumci suka bayar wajen samuwa da wanzuwa da kuma bunkasar adabin Hausa (shafi na 30). Wadannan malamai da suka rayu tun wajen karni na 17 su ne su: Wali danmarina a Katsina da Abdullahi Sikka a Kano da kuma Wali danmasani na Katsina. Bugu da kari, akwai bayani game da bayyanar masu jihadi da irin gudunmowar da mutane irin su Nana Asma’u da sauransu suka taka a fagen bunkasar adabin Hausa. (shafi na 35). Haka kuma a dai wannan babin, marubuciyar ta yi bayani game da takaitaccen tarihin rubutaccen wasan kwaikwayo na Hausa (shafi na 58).
A babi na uku, an yi bayani kan shigowar wasan kwaikwayo kasar Hausa (shafi 66 zuwa 79). Babi na hudu kuwa ya yi nazari ne kan bunkasar wasan kwaikwayo ta hanyar bayyana matallafa wasan kwaikwayo, wadanda suka kunshi fassara da baddalawa da dandamali da sauransu (shafi 80 zuwa 88).
Amma a babi na biyar, marubuciyar ta yi waiwaye ne wanda Hausawa ke cewa shi ne adon tafiya. Ta yi wannan waiwaye ne don yin tsifa da tazar irin gudunmowar da Turawan mulkin mallaka suka bayar a fagen samuwar wasan kwaikwayo da habakarsa. Dokta Sun diaomeng ta yi cikakken sharhi kan irin gudunmowar da makarantun boko da hukumomi na musamman kamar su Hukumar Fassara da Hukumar NORLA da kamfanonin dab’i kamar su NNPC da sauransu suka bayar, wajen samuwa da bunkasar wasan kwaikwayon Hausa. (shafi 89 zuwa 98).
A babi na shida wanda ya fara tun daga shafi na 101 zuwa 107, marubuciyar ta yi tsokaci ne kan tasirin Musulunci a kan marubuta rubutaccen wasan kwaikwayo na Hausa, domin fito da irin yadda tasirin Musulunci ya nashe tunani da zukatan wasu Musulmi marubuta wasan kwaikwayo na Hausa da kuma irin yadda tasirin ya bayyana a fili cikin wadannan wasanin kwaikwayon da suka rubuta. Ta kawo misalai gamsassu daga littattafan wasan kwaikwayo kamar Jatau Na kyallu (shafi na 102) da kuma Malam Inkuntum (shafi na 105).
Babi na bakwai ya rarrabe wa mai karatu bambanci tsakanin barcin makaho da na mai ido ta yin cikakken bayani game da yadda bishiyar wasan kwaikwayo take da inuwa mai sanyi da ni’ima da kuma ’ya’ya masu zakin gaske, ta hanyar fito da cikakken muhimmancin rubutaccen wasan kwaikwayo na Hausa (shafi na 108 zuwa 114). Kadan daga cikin muhimmanci ko alfanun da wannan littafi ya bayyana na wasan kwaikwayo, sun kunshi yin gargadi da wa’azi ko ilimantarwa da kuma samar da nishadi ga masu karatu ko kallo.  
A babin karshe, wato na takwas, ta yi kokarin nade tabarmar bayananta wadanda ta shimfida a cikin wannnan muhimmin littafi ta hanyar yi wa kammalawa kwalliya da gazar da ja-girar yin bayani dalla-dalla. Sa’annan an kammala babin da kawo muhimman shawarwari kan yadda za a ci gaba da taskace da kuma bunkasa adabin wasan kwaikwayon Hausa (shafi na 115 zuwa 117).
A karshen littafin, marubuciyar ta kare da sanya rataye, a inda ta kawo hotunan wasu muhimman bangayen littattafan zube da na wasu mashahuran littattafan wasan kwaikwayo na Hausa, kamar Shehu Umar da Malam Inkuntum da Iliya dan Mai karfi da Sid Hausa Plays da sauransu (shafi 348 zuwa 356). Ratayen ya yi ma’ana sosai, don yana kunshe da bayanai a kan shekarar da aka rubuta duk littafin da aka sanya bangonsa, sannan kuma an samar da cikakken sunan marubucin kowanne littafi da sunan kamfanin da ya wallafa shi da kuma shekarar wallafar, don saukaka wa masu nazari da bincike musamman wadanda suke a nesa wato kasashen ketare.  
A karshe ina da yakinin cewa duk da ’yan kura-kuren da ba a rasa ba na ka’idojin rubutu a-nan-da-can, littafin taska ce wadda ta zama zakaran gwajin dafi a fagen nazarin adabin wasan kwaikwayon Hausa. Haka kuma ko shakka babu littafi ne da zai taimaka wa dukkan daliban adabin Hausa da malamai da manazarta da marubuta da makaranta da masu bincike a kan adabin Hausa na kusa da na nesa.
A nan nake shawartar duk wanda har yanzu harshensa bai kai ga dandanar zumar ilimin da wannan littafi ya yi mana guzuri daga kasar Sin ba, to yana da kyau matuka da ya yi haramar yin hakan a kan kari.
Khalid, marubuci, manazarci kuma malamin makaranta ne da ya aiko mana sharhin nan daga Kano