Ana zaman zullumi a yankin Jukunawa na Jihar Taraba, musamman ma a garin Wukari, bayan da wani sabon fadan kabilanci ya barke tsakanin kabilun Tibi da Jukun.
Mayakan sa-kai na kabilar Jukun ake zargi da kai wani harin ranuwar gayya a wani garin ‘yan kalilar Tibi mai suna Joota wanda ke kan iyakar Jihar Taraba da ta Binuwai.
Shaidu sun fada wa wakilin Aminiya cewa an kona gidaje sama da 1,000, an kuma halaka ‘yan kalilar Tibi uku, sannan aka kashe yan Jukunawa masu yawan gaske.
A ‘yan kwanakin nan kabilun biyu, wadanda ba sa ga maciji da juna, sun kai wa juna hari da manyan makamai.
- An yi garkuwa da mutum 7 lokacin da ake maraba da Gwamnan Taraba
- An sako tsohon shugaban ma’aikatan Taraba bayan biyan Naira miliyan 20
Wata majiya a yankin ta shaida wa Aminiya cewa an raunana soja daya da dansanda daya a lokacin fadan.
Shugaban karamar hukumar Wukari, Mista Adigrace Daniel, ya ki yarda ya yi magana da wakilin Aminiya a kan wannan lamari.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Taraba, DSP David Misal, ya ce inda ake zargin an kai harin a cikin jihar Binuwai ne saboda haka ba zai ce komai a kai ba.
Shi ma kwamandan Birged ta 93 ta rundunar sojin kasa ta Najeriya dake garin Takum, Laftanar Kanar I. Sule ya ce ba zai yi magana a kan wannan lamari ba har sai ya samu umurni daga na sama da shi.
Rikice-rikice tsakanin Tibi da Jukunawa da suka ki ci suka ki cinyewa a jihohin Binuwai da Taraba dai sun yi sanadin salwantar rayukan daruruwan mutane da dukiya mai dimbin yawa.
A bara wata kungiya mai zaman kanta da ke fafutukar tabbatar da zaman lafiya a Yammacin Afirka mai suna WANEP ta ce zuwa watan Satumba akalla mutane 600 ake kashe a rikice-rikicen.