Wata tankar dakon ruwa ta take wasu kananan yara mata biyu har lahira a unguwar Kwarkota da ke Dutsen-Kura Gwari a garin Minna, babban birnin Jihar Neja.
Kananan yaran sun gamu da ajalinsu ne a ranar Laraba a yayin da motar da ta kawo wa mazauna yankin ruwa take yin ribas, ta bi ta kansu bisa kuskure.
- NAJERIYA A YAU: Tsutsa Ta Sa Kudin Kwandon Tumatir Kaiwa N20,000 A Kano
- Yadda sojoji suka ragargaji ISWAP da Boko Haram A Borno
Aminiya ta gano cewa wani bawan Allah a unguwar ne ya dauki hayar tankin ruwan domin samar da ruwan sha kyauta ga mazauna yankin, bayan matsalar rashin ruwan sha da suke fama da ita ta kara tsanani.
Wani dan unugwar, Ahmed Isyaku, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Mun jima muna fama da matsalar rashin ruwan sha a nan yankin.
“Shi ne wani bawan Allah ya dauki tankin ya kawo masa ruwa da mutanen unguwar, amma aka yi rashin sa’a, a lokacin da direban motar yake yin ribas, ya take wasu kananan yara mata, nan take rai ya yi halinsa.”