Wata tankar mai makare da fetur ta yi hatsari a kan Babbar Hanyar Maraba zuwa Abuja.
Ganin man da motar ta dauko yana tsiyaya babu kakkautawa a kan titi ya sa mazauna da masu kantuna da ke kusa da hanyar gudun tsira da rayukansu.
- An kama matashi da sassan jikin dan Adam
- An kama ’yan damfara masu kwaikwayon muryar aljanu a Katsina
- Biyan kudin fansa ga masu satar mutane haramun ne —Farfesa Maqari
A hannu guda kuma, wasu bata-gari sun rika amfani da yanayin wurin satar kaya daga kantunan da masu su suka tsere.
Wani ganau, Hassan Abdulkareem, ya ce tankar man ta kwace ne a yayin da direbanta ke kokarin kauce wa wani rami a daidai mahadar Mopol Junction da ke Mararaba a Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.
“Abin ya faru ne ranar Litinin da dare, kuma kasancewa motar ta dauko fetur, sai man da ke tsiyaya daga motar ya rika gangarawa zuwa shaguna da gidajen da ke yankin.
“Hakan ta sa yawancin masu kantuna da mazauna yankin kwashe kayansu saboda tsoron tashin wuta daga man da ke tsiyaya,” inji shi.
Ya kara da cewa tuni jami’an kwana-kwana tare babbar hanyar domin shawo kan abin da ka iya biyo baya.