✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tanade-tanaden tsaro da shari’o’i masu zafi da Kotun Ƙoli za ta warware

Hukuncin da ya shafi zaben Kano abu ne da ake ta tafka muhawara a kusan kowane kwararo da sako.

Jami’an tsaro sun yi shirin ko ta kwana yayin da Kotun Ƙoli a wannan Juma’ar za ta raba gardama kan shari’o’in zaben gwamnoni takwas.

Kotun Ƙolin dai na da jan aiki a gabanta, saboda hukunce-hukunce na shari’o’in zaɓukan gwamnan da aka ɗaukaka wadanda ke da matuƙar muhimmanci ga jihohin da abin ya shafa da kuma siyasar Najeriya.

Matakin kuma shi ne na ƙarshe ga fafutukar mulki ta hanyar shari’a, tsakanin ’yan siyasa da jam’iyyunsu, tun bayan zaɓukan 2023.

Hukunce-hukuncen shari’o’in zaɓen gwamna da ƙananan kotuna suka yanke a baya, ba su iya kawo ƙarshen ja-in-jar da ake ta bugawa ba.

Sai dai yanzu, an zo magaryar tiƙewa. Kotun da ake kira ‘Daga Ke Sai Allah Ya Isa’, za ta yi fashin baƙin dokoki, sannan ta zartar hukunci.

Bisa wannan dalili ne masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro suka yi tanadin matakai domin fargabar abin da ka iya zuwa ya komo musamman idan aka yi la’akari da yadda dole akwai bangaren da hukuncin Kotun Kolin ba zai yi wa daɗi ba.

Jihohin da wannan lamari ya shafa sun hada da Kano, Filato, Legas, Zamfara, Bauchi, Kuros Riba, Abia da Ebonyi.

Jihar Kano

A Jihar Kano dai, Aminiya ta ruwaito cewa hukuncin da ya shafi rigimar gwamna a jihar abu ne da ake ta tafka muhawara a kusan kowane kwararo da sako.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammadu Usaini Gumel, ya shaida wa manema labarai bayan ganawa da wasu shugabannin tsaro, cewa suna da isassun ma’aikata da za su iya tunkarar duk wani abu da zai bijiro.

“Mun tanadi isassun jami’ai da za su samar da tsaro a dukkan wuraren da suka hada da ofisoshin jam’iyyun siyasa, gidan gwamnatin jihar, hedkwatar INEC, Bankunan da wuraren kasuwanci, Masallatai, Majami’u, wuraren shakatawa da tashoshin motoci.

CP Gumel ya yi karin haske da cewa ba a buƙatar sanya dokar hana fita, yana mai gargadin cewa hukumomin tsaro ba za su bari bata-gari su fake da bayyana farin cikin sakamakon Kotun Ƙolin ba wajen wawure dukiyar mutane ba.

Filato

A Jihar Filato kuwa, rashin tabbas da kyakkyawan fata na ci gaba da fuskantar juna cikin zukatan mazauna jihar musamman a tsakanin magoya bayan jam’iyyu yayin da ake dakon hukuncin da Kotun Ƙolin za ta yanke

Wakilinmu da ya zagaya tsakiyar birnin na Jos, ya ruwaito cewa an ga sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a cikin motoci suna rangadi domin bai wa mazauna kwarin gwiwar irin tanadin da aka yi a bangaren tsaro.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Okoro J. Alawari, a ranar Litinin din da ta gabata ya tabbatar wa mazaunan zaman lafiya a lokacin yanke hukunci da bayan an yanke, inda ya yi kira ga kowa da kowa da su ba ‘yan sanda hadin kai.

Jerry Nungi, wani mazaunin Jos, ya ce, “Ina da yakinin za a zartar da hukunci ba tare da wani tashin hankali ba. Mun ga yadda aka yi tanadin tsaro a ko’ina kuma muna fatan babu wani mummunan abu da zai faru.”

Zamfara

Da yake zantawa da Aminiya, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da cewa an tanadi duk wasu shirye-shirye domin kare rayuka da dukiyoyi kafin yanke hukunci da kuma bayan yanke hukunci.

Ya ce: “Mun tura jami’an mu zuwa wurare masu mahimmanci a cikin babban birnin jihar da kuma manyan garuruwa.

“Mun shirya tsaf domin dakile duk wani yunkuri na kawo cikas ga zaman lafiya da zaman lafiya da ake samu a jihar.”

Haka kuma, an tura sojoji dauke da muggan makamai zuwa gidan tsohon gwamnan jihar, Muhammad Bello Matawalle da ke kan titin Gusau da sauran wurare a cikin babban birnin jihar.

Legas

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce sun yi tanadin isasshen tsaro domin tabbatar da cewa ba a karya doka da oda gabani da kuma bayan hukuncin Kotun Kolin ba.

“Ba ma tsammanin za a samu wata matsala a Legas, amma duk da haka mun dauki matsayi da  matakan da suka dace saboda Kwamishinan ‘yan sanda, CP Adegoke Fayoade ya ba da umarnin a jibge karin jami’an tsaro a kan tituna.

“Bayan haka, ya kuma ba da umarnin kara ganin ’yan sanda a kusa da manyan cibiyoyin gwamnati, wuraren da aka san ba wutya tarzoma ta tashi”, in ji PPRO.

Kuros Riba

Shi dai Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kuros Riba, Grimah Gyogon ya ce ba kasafai suke bayyana dabarunsu na dakile laifuka ko tashin hankali ba.

A cewarsa, “Hukumarmu ta riga ta yi la’akari da tanadin duk ababen da suka dace,” in ji shi.

Wani shugaban al’umma a Karamar Hukumar Calabar ta Kudu, Ekamba Cobham, ya ce babu wani tashin hankali a jihar gabanin hukuncin da kotun kolin ta yanke.

Shari’o’i masu zafi da Kotun Ƙolin za ta warware

Abba da Gawuna

Ɗaya daga cikin shari’o’in zaɓen gwamna mafi zafi da Kotun Ƙolin za ta yanke hukunci, ita ce ta Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna.

Shi dai Abba Kabir yana ƙalubalantar soke nasarar zaɓensa ne da ƙananan kotuna suka yi a baya.

Tun da farko, kotun zaɓen gwamnan Kano a watan Satumban 2023 ce ta soke ƙuri’’a 165,633 wadda in ji ta, aka yi wa ɗan takarar na jam’iyyar NNPP aringizo, bayan hukumar zaɓe a watan Maris, ta ce ya samu ƙuri’a 1,019, 602.

Kuma ta umarci hukumar INEC ta ƙwace shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba, sannan ta bai wa ɗan takarar jam’iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna shaidar zama zaɓaɓɓen gwamna.

Gwamna Abba dai bai gamsu da hukuncin ba, don haka ya wuce zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Sai dai, ita ma kotun ɗaukaka ƙarar karkashin jagorancin mai shari’a Moore A. Adumein ta bai wa jam’iyyar APC nasara bisa hujjar cewa Abba ba ɗan jam’iyyar NNPP ba ne lokacin da aka tsayar da shi takara, don haka ta nemi a rantsar da ɗan takararta Nasiru Gawuna.

Dangane da batun kasancewar Gwamna Abba dan jam’iyyar NNPP, lauyan INEC Abubakar Mahmoud (SAN) ya bayyana wa Kotun Koli cewa al’amarin cikin gida ne na jam’iyyar siyasa, inda ya ce ba batun tsarin mulki ba ne kamar yadda jam’iyyar APC ta yi ikirari, wanda ya yi nuni da sashe na 177 (c) na kundin tsarin mulkin kasar, wanda aka yi wa kwaskwarima, da kuma Sashi na 77 na Dokar Zabe.

Kazalika, lauyan gwamnan, Wole Olanipekun (SAN) ya bayyana cewa batun kasancewar Gwamna Yusuf na jam’iyyar NNPP lamari ne da ake iya bijiro da shi kafin zabe kuma kotun daukaka kara ba ta da hurumin sauraronsa.

Matawalle da Dare

Tamkar APC ta Bello Matawalle, Gwamna Dauda Lawal Dare ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli yana neman ta tabbatar da nasararsa, wadda kotun baya ta soke, har ma ta ba da umarnin a yi sabon zaɓe cikin wasu ƙananan hukumomi.

Alƙalan kotun ɗaukaka ƙarar sun ce za a gudanar da zaɓen ne a ƙananan hukumomin Birnin-Magaji Bukkuyum da kuma Maradun, saboda a watan Maris ɗin 2023, ko dai ba a yi zaɓe a wuraren ba, ko kuma an yi zaɓen amma ba a ƙidaya sakamakonsu ba.

Hukumar zaɓe dai a lokacin ta ayyana ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Dauda Lawal a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’a 377, 726, inda a wani lamari mai cike da ban mamaki, ya kayar da gwamna mai ci Bello Matawalle.

Sai dai ɗan takarar na APC, Bello Matawalle wanda yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaron Najeriya, ya zargi Inec da kassara nasarar da ya samu, saboda ta gaza haɗawa da sakamakon wasu mazaɓu.

Kotun sauraron ƙarar gwamnan Zamfara a ranar 18 ga watan Satumba ta yanke hukunci a kan shari’ar, amma ba ta ba shi gaskiya ba, a cewarta ƙarar da ya shigar gabanta, ba ta da tushe. Kuma ta tabbatar da zaɓen Gwamna Dare.

Lamarin da ya sanya Matawalle garzayawa kotun ɗaukaka ƙara, wadda ita kuma ta ba shi nasara. Sai dai Dauda Lawal Dare ya ce bai yarda ba.

Mutfwang da Goshwe

Shari’ar Caleb Mutfwang da Nentawe Goshwe daga jihar Filato, na ɗaya daga cikin shari’o’i masu zafi, da ake sa ran kotun ƙolin a Juma’ar nan, za ta yanke hukunci a kai.

Gwamna Mutfwang ya garzaya gaban kotun ne bayan kotun ɗaukaka ƙara a watan Nuwamba ta rusa zaɓensa, inda ta umarci Inec ta bai wa abokin shari’arsa shaidar cin zaɓen watan Maris.

Yana roƙon kotun ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ta jihar Filato, kuma ta jingine hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, saboda a cewarsa, masu ƙarar ba su da ‘yancin ƙalubalantar yadda wata jam’iyya ta zaɓi shugabanninta na jiha.

Yayin da Nentewe Goshwe na jam’iyyar APC yake fatan kotun ƙoli za ta jaddada hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya ba shi nasara.

Kowanne a cikin ɓangarorin biyu, yana bayyana ƙwarin gwiwar cewa hukuncin na Juma’a, shi zai bai wa nasara.

Bala da Saddique

A nan ɗan takarar jam’iyyar APC a Zaɓen Gwamnan Jihar Bauchi na 2023, Saddique Abubakar ya sake maka Gwamna Bala Mohammed na PDP, ƙara a gaban kotun ƙoli.

Tun da farko, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ta Jihar Bauchi da kotun ɗaukaka ƙara duk sun kori ƙararsa, suna cewa ba ta da tushe.

Saddique Abubakar dai yana tunƙahon cewa takardun zaɓe masu yawa da aka yi amfani da su, ba a cike su yadda ya kamata ba. Sannan ya yi zargin cewa ba a yi biyayya ga kundin dokokin zaɓe a lokacin kaɗa ƙuri’ar zaɓen gwamna a Bauchi ba.

Sai dai, kotun ɗaukaka ƙara ta ce ɗan takarar na APC ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji da shaidu da za su tallafi zarge-zargensa.

Duk da haka, bai yi ƙasa a gwiwa ba, a Juma’ar nan Saddique Abubakar yana fatan kotun ƙoli za ta yi hujjojin da ya gabatar duban basira, kuma ta ba shi gaskiya, yayin da abokin takararsa na PDP ke fatan alƙalan kotun kamar takwarorinsu na kotunan baya, su kori wannan ƙara.