Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da umarnin rufe makarantun kwana 16 da ke wajen gari a kan iyaka a fadin Jihar Sakkwato.
Wannan umarnin ya biyo bayan taron Majalisar Tsaron jihar karo na 17 da aka gudanar a ranar Laraba, 16 ga watan Dasumban 2020.
- Gwamnatin Katsina ta karyata labarin sako Dalilan Kankara
- Gwamnonin APC sun taya Buhari murnar cika shekaru 78 a duniya
Kwamishinan Ilimi, Bello Muhammad Guiwa ne ya sanar da hakan a wata takarda da aka aika wa manema labarai, wadda Mai Ba Gwamna Shawara a Harkokin Yada Labarai, Muhammad Bello ya sanya wa hannu.
Jerin makarantun da aka zayyano umarnin ya shafa sun hadar da:
- Sakandaren mata ta Illela
- Sakandaren Arabiya ta Sultan Muhammadu Tambari da ke Illela
- Kwalejin Mata ta Gamji da ke Rabah
- Sakandaren mata ta GSS Gada
- Sakandaren mata ta GSS Gandi
- Sakandaren mata ta GSS Goronyo
- Sakandaren mata ta GSS Isa
- Sakandaren mata ta GSS Sabon Birnin Gobir
- Makarantar Kwana ta Firamare da ke Isa
- Makarantar Firamaren Kwana da ke da kuma ta Jabo.
- Karamar Sakandare ta Sabon Birni
- Sakandaren mata ta GSS Kebbe
- Sakandaren mata ta GSS Tureta
- Makarantar Fasaha ta Gwamnati da ke Binji
- Kwalejin Fasaha ta Olusegun Obasanjo da ke Bafarawa.
Sanarwar ta ce rufewar ta wucin gadi ce na tsawon sati biyu, inda aka bukaci shugabannin makarantun su bi umarnin da aka shata.