✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyin tsaron mutuncin Uwargida (2)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku game da tsaron mutuncin Uwargida a gidan…

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku game da tsaron mutuncin Uwargida a gidan mijinta. Da fatan Allah ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Tambaya Ta 2:
Don Allah ku yi bayani ga matan aure kan yadda za su tsare mutuncinsu a kafofin sadarwar zamani (social media), musamman yadda suke shiga guruf-guruf da ke cakude da maza, kuma su yi ta surutu da mazan, da rubuta kalmomi irin su murmushi da dariya da murguda baki da gatsine da daga gira da harara da dai sauransu. Ni ina ganina bai kamata matar aure ta rika rubuta ire-iren wadannan kalmomi ba ga mijin da ba nata ba.
Barista KD
Amsa: Malam Barista ai ba matan aure kadai ba, har wadanda ba su da auren ma bai kamata su rika rubuta irin wadannan kalamai a cikin taron mazajen da ba muharramansu ba. Wadannan kalamai ne da in mace ta yi su za su kayatar da namiji su sa masa nishadi a zuciya; kuma mace mai mutunci, mai kamun kai ba ta zuwa cikin taron maza tana kayatar da su da murmushinta, ko ta nishadantar da su da gatsinenta, ko ta sanya tsigar jikinsu na tashi da daga girarta. Mace mai kamun kai; mai mutunci, to mijinta kadai take nishadantarwa da kayatarwa, shi kadai ne take nishadantuwa da hirarsa. Don haka mata masu irin wannan hali ya kamata su tuba su daina; su sani cewa wannan ko kusa bai yi kama da halayen macen kirki mai kamun kai ba. Kuma ’ya mace ba ta da abin da ya kai rikon mutuncinta tsada da muhimmanci a rayuwarta, don haka ku yi wa kanku fada domin ceto mutuncinku tun da sauran darajarsa.
Tambaya Ta 3:
Assalamu Akaikum. Don Allah Anti Nabila ki ba ni wasu shawarwarin ko ka’idojin da matar aure za ta yi amfani da su don ta tsare mutuncinta a facebook. Ina son in fara amfani da shi sosai domin ’yan uwana da abokaina kowa na yi. Amma maigidana ya hana ni saboda wai ana cakuduwa da mazan da ba muharramai ba.
Nagode, Ummu Sulaiman.
Amsa: Maigidanki kam ya yi gaskiya; lallai ana cakuduwa da kuma kulla dangantaka tsakanin maza da matan da ba muharraman juna ba a facebook da ma sauran kafofin sadarwa, amma yin hakan sai ga wanda ya so, domin akwai sharudda da ka’idojin da suke ba mutum cikakken ’yancin zabar wadanda zai yi hulda da su a wadannan kafafe da kuma hanyar da yake son ya yi hulda da su. Ga shawarwarin da idan kika yi aiki da su sau da kafa, cikin yardar Allah za ki kubuta daga hadurran da ke da tattare da wadannan kafafe kuma ki amfana da su:
•    Kyautata Niyya: Yana da matukar alfanu ki kulla kyakkyawar niyya ta shiga wadannan kafofin sadarwa na zamani, watau ki yi nufin aikata alheri da sadar da alheri yayin kulla niyya. Kada ki yi niyya don kawai kina son ki shiga sabon yayi, ko don ki burge, ko don kowa na yi don haka kema sai kin yi, sai ki shiga da niyyar kiyaye dokokin Allah da kuma aikata abubuwan alheri da za su samar da lada da kauce wa aikata ayyukan sabon Allah da za su samar da zunubi.
•    Tsare Dokokin Ubangiji: Ki sani yake ’yar uwa! Kafofin sadarwa akwai abubuwan alheri da yawa kuma akwai abubuwan sharri da yawa, don haka dole ne yin taka tsan-tsan a wadannan kafofi don ganin cewa ba ki ketare iyakokin da Ubangiji Madaukakin Sarki Ya gindaya miki a matsayinki na Musulma ba.
•    Takaitawa wajen amfani: Kada ki bari amfani da wadannan kafafe ya zame miki jiki har ya kasance sun hana ki yin wasu ayyuka masu muhimmanci a kan lokacinsu.
•    Neman Ilmi: Akwai abubuwan ilmi sosai a wadannan kafafe; don haka ki mayar da su kafar neman ilmi da wayar da kai; ki mayar da hankalinki ga bangarorin karuwar ilmi da ke wadannan kafafe, musamman ta yadda za ki kyautata zamantakewa da maigidanki da tarbiyyar ’ya’yanki. Ki guji abubuwan ban dariya da bushasha domin ba za su karar da ke da komai ba.
•    Yin Da’awa: Idan kin yi amfani da su yadda suka dace, wadannan kafafe za su zama miki hanyoyin samun lada,  su iya zama sanadiyyar shigar ki Aljannah; don haka ki mayar da wadannan kafafe hanyar yin da’awa a gare ki, ta hanyar karanta abubuwan addini da suka iso gare ki, aiki da abubuwan da kika karanta da watsa su ga ’yan uwa da abokan huldarki.