Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Saboda karin tambayoyin da muka samu masu nasaba da bambancin sha’awa tsakanin ma’aurata, insha Allahu za mu ci gaba da bayani kan wannan matsala da hanyoyin da za a bi don gusar da ita da dakile tasirinta cikin zamantakewar ma’aurata.
Tambayoyi masu nasaba da gamin gambiza
1. Mijina ba ya gamsar da ni, mun nemi magani har yanzu ba mu dace ba.
2. Ni ina da mata, mun yi shekaru da ita amma wajen ibadar aure nan da nan sai ta gaji, don Allah a taimaka mini da shawara.
3. Don Allah a taimake ni ina da matsala ba na jin sha’awa, mijina sai dai ya yi ta yi mini na dole.
4. Me ke sa idan ina tare da mijina ba ni jin dadi kuma me ke sa mijina yake saurin kawowa?
Tambayoyi masu nasaba da yin ibadar aure fiye da sau daya a rana:
5. Na kasance ba na iya yin ibadar aure fiye da sau daya a rana maidakina kuma tana bukatar fiye da haka. Yaya zan magance wannan matsala?
6. Ni matata ke mini korafin ban gamsar da ita kuma in na sha maganin karfin maza yana sa mini ciwon kai. Ina mafita?
Wasu daga cikin sababbin tambayoyin da suka iso wannan fili game da wannan matsala. Da fatan Allah Ya daidaita tsakanin ma’aurata ta kowace fuska, amin.
Gamin gambizar sha’awa tsakanin ma’aurata wani yanayi ne da ke faruwa duk lokacin da aka samu bambancin yanayin sha’awa a tsakanin ma’aurata. Gamin gambizar sha’awa na da kofofi da dama ta inda take kunno kai cikin rayuwar ma’aurata, misali, bambancin karfin sha’awa, bambancin yawan bukatuwar sha’awa da bambancin lokutan motsuwar sha’awa. Ko bambancin lokacin gabatarwa, yanayin gabatarwa da kuma bambacin abubuwan yi lokacin gabatarwar. Duk ta inda wannan matsala ta bullo, to ta kan jefa daya ko duk ma’auratan cikin wani irin hali na kunci da kaka- ni- ka- yi.
Mata ne suka fi cutuwa da wannan matsalar a cikin rayuwar aurensu sama da maza saboda kasancewar matsayin mace da irin rawar da take takawa cikin rayuwar aure. In maigida ya fi uwargidansa yawan bukatuwar sha’awa, dole ne ta yi ta hakuri tana yi ba tare da tana jin dadin yin ba, mafi yawan lokuta ma maigidan bai san irin sadaukarwa da uwargidansa ke yi ba wajen ba shi hakkinsa. Matan aure da yawa na fadar yadda suke ibadar aure don kawai su fita hakkin mazansu:
“Tun da na yi aure ban taba jin dadin ibadar aure ba, yanzu ina da ’ya’ya bakwai, kuma kullum ina cikin fargabar yi, me ke kawo irin haka?”
“Ba na jin sha’awa lokacin ibadar aure da mijina, ko me za mu yi ba na jin komai.”
“Ina da matsala da maigidana, saboda bai yin wasa kafin ibadar aure, ni ko sai ina jin zafi, koyaushe ji nake kamar ranar farko, hakuri kawai nake yi. Kuma ina son wasan, shi ne ba ya so. Mece ce shawara?”
Haka nan in aka yi rashin dace uwargida ta fi maigidanta bukatuwa da sha’awa, to a nan ma wahalar ta fi yawa, domin bayan halin kuncin hakan, wannan matsalar na kai wadansu ga aikata ayyukan sabo garin neman mafitar sha’awar u:
“Mijina ba ya son kusanta ta da ibadar aure, sai mu yi wata uku zuwa hudu kuma ni ina bukatarsa, yaya zan yi don Allah?”
“Don Allah Anti Nabila ki kara kira ga maza su rika kokari suna biya wa matansu bukatunsu na sha’awa lokacin ibadar aure. Saboda ni dai ban yi dacen miji ba ta wannan fanni, ya wadata ni da dukan kayan kyale-kyalen jin dadin rayuwar duniya, amma a shekara bai fi ya kula ni sau uku ba. Na yi kuka har na gaji, na yi masa nasiha ba iyaka, amma duk ba canji, Wallahi Anti gab nake da in shiga wani hali, domin ni mace ce mai tsananin bukata, ki taimake ni da shawara don Allah.”
Sannan su ma mazan suna cutuwa da shiga halin kaka-ni-ka- yi, in Allah Ya yi matan da suke aure ba masu hakuri ba ne balle har su daure su sadaukar da nasu jin dadin don faranta wa mazansu:
“Duk lokacin da muke tare da matata, ba ni da ikon taba jikinta sai ta ture hannuna, kuma ita har mu gama ibadar aure ba za ta taba jikina ba, ba ta son a yi wasanni ko kadan, kuma ba ta jin nasiha. Wannan abin yana damuna, a taimaka mini da shawara.”
“Me ke sa wadansu matan sai su rika nuna kamar an matsa musu a duk lokacin da aka neme su, ko su fadi wata bakar magana har mutum ya ji ya fasa? Yaya za a gane irin wadannan mata don a kauce musu, kuma in mutum ya riga ya yi aura mene ne mafita? Domin irin wannan ya sha kashe aure kuma a rasa dalilin mutuwarsa.”
Sai mako na gaba sauran bayani na zuwa insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.