Na dade ina fama da ciwon tsargiya kuma har yanzu ban samu magani ba. Mece ce illar hakan? Kuma mece ce shawara?
Daga Abdulmajid, Auchan
Amsa: Abubuwa da dama kan kawo tsargiya ko fitsarin jini. Ciki har da shigar kwayoyin cuta masu makalewa a tantanin fitsari, wadanda aka fi kwasa a wankan kududdufi, ko shigar kwayoyin ciwon sanyi, wanda wasu mazan kan sa wa mata, ko kuma mata ke sa wa maza. Su wadancan kwayoyin cuta na kududdufi wato schistosoma, har kari za su iya kawowa a marar, alamun karin kuma har akwai mutum ya rika ganin fitsarin jini.
Ban da kwayoyin cuta akwai dattin fitsari da kan dunkule su zama ’yan tsakuwowi sukan sauko daga koda, su taru a ita marar fitsarin, su rika kawo tsargiya. Akan iya samun kuma matsalar kodar ma ita kanta ta kawo fitsarin jinin.
Ka ga ke nan idan ba a asibiti kake neman magani ba, ba za a san daga ina matsalar take ba. A asibitin ma, idan ba yi a maka gwaje-gwajen fitsari da hotunan mafitsara ba, kai ma ka san ba a dauki hanyar magance matsalar taka ba.
Ni kuma ina so na san irin kwayoyin cutar da kan taba koda. Ko matsalar na warkewa kuwa?
Daga Musa A.
Amsa: E, kamar yadda muka yi dan bayani a sama, kwayoyin cuta daga kasan mafitsara suke shiga su yi sama su nufi koda. Akan same su ko a wanka a gurbataccen ruwa, ko ta ciwon sanyi wanda mace kan sa wa namiji, ko namiji ya sa wa mace, ko a tsarkin hoge maras tsabta da dai sauransu. Ba kamar tsakuwa ba, wadanda suke saukowa daga koda, wasu ma su makale a kodar, su kwayoyin cuta hawa suke daga kasa su nufi kodar su kawo mata matsala. Mata sun fi maza yawan samun irin wannan matsala, saboda hanyar mafitsararsu gajeriya ce kuma idan maigida, mai mata uku yana dauke da kwayar, kusan duk sai ya raba musu. Don haka ta nan za a ga akwai ’yar alakar ciwon sanyi da ciwon mafitsara.
Alamomin shigar kwayoyin cuta a koda sun hada da fitsarin jini, ciwon kwibin baya, na gefen dama ko hagu, ko ma duka biyun, dangane da kodar da abin ya shafa. Wasu sukan ji yawan fitsari, amma idan suka ke sai su yi dan kadan, ga ciwon mara mai tsanani yayin fitsarin a wasu lokutan.
Idan aka gano wace irin kwayar cuta ce ta hanyar aunawa da gwada fitsarin, aka ba da magungunan kashe su, ana warkewa sarai.
Ni ma ina yawan fitsari sosai. Na je asibiti sai aka yi min gwajin suga, aka ce wai maki 6. To shin akwai matsala ne?
Daga Usani Munzali
Amsa: To, ai ka ga kai kuma gwajin sukari kawai aka yi maka domin ko a gano matsalar suga, ba a yi maka sauran gwaje-gwaje na fitsari da koda a ga ko akwai tsakuwa ko kwayoyin cuta ba. Amma sukari maki shida, tunda ba ka ci abinci ba a lokacin da aka yi, daidai yake, bai yi sama ba kuma bai yi kasa ba, domin da ma kamata ya yi ya zama tsakanin maki 3 zuwa 7. Na ka ya doshi bakwan, idan akwai masu ciwon suga a zuri’arka to sai ka yi taka-tsantsan.
Idan jini ya yi yawa a jiki ba zai ba da matsala ga lafiya ba? Kuma ya mutum zai gane yawan jininsa ya yi sama?
Daga Aliyu Y., Jigawa
Amsa: Ba kasafai jini kan yi yawa ba, domin shi jini yana sabunta kansa duk bayan watanni, kuma koda takan fitsarar da abin da ya wuce misali na yawan ruwan da ke cikin jini a kullum, don haka ba wasu alamu ake ji ba. Duk da haka dai a wasu lokuta akan samu wasu an je gwada jininsu an ga kwayoyin jini jajaye, wadanda su ne suke nuna yawan jini, sun yi yawa, haka kurum. A irin wadannan akan samu dan yawan ciwon kai kuma akan ba su shawarar su ba da leda daya ta jini, kwatankwacin ledar ruwa, ga asibiti don amfanin masu bukata.
Don haka idan kana ganin jininka ya yi yawa, kuma kana cikin koshin lafiya, ka je wata cibiyar ba da jini a asibiti kawai ka ce za ka ba da ledar jini. Su ne za su yi maka duk gwaje-gwajen da ya kamata na yawan jininka da na kwayoyin ciwon hanta da na ciwon kanjamau duka kyauta. Sai komai ya yi daidai ma ake daukar jinin.
Ina jin wata jijiya tana harbawa a gefen kaina kusa da kunnuwana. Ko matsala ce?
Daga Shehu Mu’azu, Funtuwa
Amsa: A lokuta da dama, idan mutum ya yi shiru a daki shi kadai zai ji yadda zuciyarsa ke buga jini a sassan jiki. Haka nan idan mutum ya kwanta a kan kunnensa na barin dama ya yi shiru, zai ji wata jijiyar jini ta wannan barin, me kai jini kwakwalwa da ta wuce ta bayan kunnen, tana harbawa. Amma haka kawai kana zaune da wuya ka ji, sai dai idan gudu mutum ya dan yi, ya dawo ya zauna. Wannan duk ba wata matsala ba ce. Sai dai kamar yadda muke ba da shawara, yana da kyau mutum ya rika auna karfin bugun jininsa a kalla sau daya a shekara, wato a duba a gani ko yana da hawan jini ko ba shi da shi.
Me ke sa hakorina ke zubar da jini da yawa?
Daga dahiru, Kura
Amsa: Kai ma ka san ba lafiya ba. Ba hakori ne ke zubar da jini ba, sai dai dasashi tunda a nan jijiyoyin jini suke, kuma alama ce ta cewa watakila akwai matsala ko dai a dasashin ko a hakori. Idan dasashi ne kawai, to ba ka cin abinci mai dauke da sinadaran bitamin sosai, idan kuma matsalar hakori ce, wato idan ya yi rami ke nan, to ka bar kwayoyin cuta sun cinye maka hakori ke nan, wanda shi kuma tsabtar baki ke kiyaye hakan. To ka dai daure ka nemi asibitin hakori a duba a san mafita.
Kafin ka samu inda za a duba ka dai, tun a yau za ka iya neman ruwan wanke baki a kyamis na chlorhedidine ka rika kurkure bakin bayan ka yi burushi ko aswaki. Ko kuma idan ba za ka iya saya ba, ka samu ruwan zafi ka zuba gishiri ka rika kurkure bakin bayan burushi ko aswaki. Sa’annan a rika cin ’ya’yan itatuwa akai-akai.
LAFIYAR MATA DA YARA
Amsoshin Tambayoyi
Likita yarinya ce ta hadiyi batirin agogo, muka je asibiti aka ce ba komai, za ta kasaye shi. Ko mece ce shawararka?
Amsa: Wannan tambaya tana da muhimmanci kwarai game da lafiyar yara. Sau da dama ana kawo wa ma’aikatan lafiya irin wannan matsala ta yara masu hadiyar wani abu. A hakikanin gaskiya da wannan matsala da kuna ta ruwa ko abu mai zafi a yara, mun fi danganta shi da sakacin mahaifiya ko mai raino.
Abubuwan da yara kan dauka su kai baki sun kasu kashi-kashi; masu hadari da marasa hadari; masu narkewa su bi jiki da marasa narkewa; masu wucewa ciki da masu tsayawa a makoshi.
Za a iya samun masu narkewa su bi jiki marasa illa ko hadari, da masu illa, kuma za a iya samun marasa narkewa, amma kuma masu hadari. Marasa narkewa ana kasayar da su. Duk wasu karafa da robobi ba sa narkewa a ciki, amma suna da hadari. Wadanda suka fi hadari su ne masu tsini ko kaifi, irin su allura ko fil ko reza, domin sukan iya yanka ko huda hanji, sai kuma masu dan girma saboda za su iya tokare abin da ke wucewa cikin hanji. A irin wannan rukuni akan samu kashi ko kayar kifi.
Duk da cewa da gaske ne ana sa ran karamin batirin agogo yakan wuce a kasayar da shi cikin ’yan kwanaki, abin da asibitin ya kamata su yi shi ne hoton ‘dray’ na duka jikin yarinyar a gani ko ina batirin ya shiga, yana wuya ne ko yana ciki, yana babban hanji ne ko karamin hanji. Idan yana makale a makogwaro akwai matsala babba, amma idan a ciki ko hanji aka hango shi, akan ba da ’yan kwanaki sa’annan a sake hoton. A hoto na biyu yawanci ba a ganinsa alamar cewa an kasayar. Wata babbar shaida kuma ita ce ta bin bayan-gidan yarinya duk lokacin da ta yi a duba a ga ko batirin ya fito.
Shin ya dace a yi wa yaro shayi daga haihuwarsa a likitance?
Daga Usman B., Ningi
Amsa: A’a, a likitance akan ba da ’yan kwanaki kafin a yi wa yaro shayi domin a ga yadda fitsarinsa da yanayin mafitsarar yake, domin wasu fatar da ake yankewa ma ba su da ita, wasu kuma suna bukatar fatar domin wani dan gyara ga wata ’yar matsala da kan shafi wasu jariran maza, wadda takan sa kofar fitar fitsarinsu a sama ko a kasa, maimakon a tsakiya. Ko ma dai mene ne dai, dole an fi so likita ya duba mafitsarar sosai kafin ya ce za a iya yin shayi ko a’a.