✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tamabayoyin Duniyar Ma’aurata 2

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Insha…

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Insha Allah za mu ci gaba da amsa tambayoyin da masu karatu suka aiko masu nasaba da bayanan da suka gabata kan hanyoyin farfado da soyayya tsakanin ma’aurata.

Tambaya 2

Ina neman shawara mijina gaba daya bana birgeshi, duk abin da na yi sai ya ce ranshi ya baci wai ban iya magana ba, don Allah a ban shawara.

Amsa

To ga shawarwari:

1.    Akwai tsammanin ke baki da ko wace irin matsala iyaka shi maigidanki ne yake ji kamar kin ci gabansa da yawa shi ya sa yake kokarin koda yaushe ya ga ya kankantar da ke: Masana kimiyyar halayyar dan Adam sun bayyana cewa duk mutumin da ya cika yawan kushe da nuna ba dai-dan wasu ko yawan kankantar da wasu to a hakikanin gaskiya kanshi yake kushewa kuma shi ne can cikin kashin ranshi bai san martaba da kimar kanshi ba sai yake sauke nakasunsa a kan wasu musamman makusantanshi kamar mata da ’ya’ya. Don haka ki kwantar da hankali; sai ki dage da yi masa addu’ar Allah Ya ganar da shi ya gyara masa wannan aibun da ke cikin halayyarsa da mu’amalarsa.

2. Kin san kanki sama da yadda kowa ya sanki, mene ne ra’ayinki game da wannan ikirarin da maigidanki yake yi? Shin kina jin lallai ba ki burge shi din? Lallai ba ki iya magana ba? Amsar da hankalinki ya ba ki ki yi aiki da shi, shi ne daidai ki goge wancan ikirari da maigidanki yake yi kuma ki yi ta addu’a Allah Ya gyara masa yanayin mu’amalarsa.

3. Ki yi dubi cikin mutanen da kika zauna da su, iyayenki, ’yan uwanki, makwabta, kawaye da sauransu, in har ba wanda ya taba nuna maki cewa ba ki iya magana ba to sai ki fahimci cewar matasalar daga nakasun maigidanki ne na rashin iya mu’amala, sai ki kwantar da hankalinki ki ci gaba da hakuri da yi masa addu’a.

4.    In kuma akwai wanda koda a kaikaice ya nuna miki irin yadda maigidanki yake nunawa to sai ki yi azamar ganin kin gyara wannan nakasun naki ta hanyar:

• Rage yawan surutu in kina yi, domin yawan magana shi ke sa har a fadi magana mara dadi ko mara ma’ana.

• Sannan ki sa ido in mutanen da kike ganin sun iya hira suna magana ki lura da irin yadda suke yi kina koyo a hankali.

•      Babban sihirin iya hira shi ne yawan saurare ya fi yawan magana; ki rika yin shiru kawai kina saurarensa kina ba da ’yar karamar amsa inda ya dace jefi-jefi kamar eh, a’a, haka ne, kwarai kuwa da sauransu.

• In kuma shi ne ya tambaye ki wani abu ki ba shi daidai amsar tambayarsa ba ragi ba kari, kada ki zarce ki wuce ki yi ta ratata abubuwan da ba sa cikin tambayarsa da sauransu.

• Babban sirrin dai ki kama baki daga yawan magana, ki bar fuskarki da jikinki su rika bayyanar da wasu abubuwan ba komai ne sai kin buda kin fada ba.

• Ki lura da irin abubuwan da in kin yi su yake yin mita sai ki yi kokari ki guje musu don dai a zauna lafiya kuma ki kara gyara hanyar shiga Aljannarki.

Nasiha ga maigidanki dama sauran magidanta masu irin wannan halin: wannan halayya ta yawan kushe da kankantarwa da mitar kananan abubuwan da ba su kai sun kawo ba sun saba wa koyarwar addinin Musulunci, ko da a ce da gaske din ne matarka ba ta  burge ka, da gaske din ne ba ta iya magana ba,  ba daidai ba ne ka rika yawan kushe ta da yawan nuna bacin rai da sauransu; aiki da hankali shi ne sai ka danne ka bar abin a zuciyarka, cikin wayo da dabara ka rika hankaltar da ita: “ba haka za ki yi ba, a’a haka za ki yi, kaza za ki ce ba kaza za ki ce ba da sauransu, ko ka zaunar da ita cikin sanyin rai ka yi mata nasiha mai cike da kwatanci da misalai. A yankin karshen aya ta 19 cikin Suratul Nisa’i’ Allah Madaukakin Sarki Ya yi umarni ga magidanta:

…Kuma ku yi zamantakewa da su da alheri; Sa’annan idan kun ki su, to akwai tsammanin ku ki wani abu alhali kuwa Allah Ya sanya alheri mai yawa a cikinsa.”

Babu alheri a cikin yawan kushe da nuna aibu da kasawar matarka a koyaushe.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Musulmi shi ne wanda Musulmi suka kubuta daga cutarwar hannuwansa da harshensa.”

Akwai tangarda a cikin Musuluncin mutumin da yake yawan aibata mutane da bakinsa; kowa yana da nakasunsa kuma kowa yana da kamalarsa; cikakken mutum Musulmin kwarai shi ne wanda zai kau da kansa daga nakasu ya mai da hankalinsa ga kamala.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.