✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin N8K: Tinubu ya sauya shawara

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin yin garambawul ga shirinsa na raba N8,000 ga matalauta domin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur. Kakakin…

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin yin garambawul ga shirinsa na raba N8,000 ga matalauta domin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur.

Kakakin shugaban ƙasa, Dele Alake ya ce shugaban ya sauya shawara kan shirin ne sanadiyyar sukan da yake sha daga  ƴan Najeriya.

Tuni dai Majalisar Dattawa ta sahhalaewa Gwamnatin Tarayya raba N8,000 ga matalauta miliyan 12 tsawon watanni shida.

Abubuwan da za a iya yi da kudin tallafin man fetur na wata daya da aka cire

Majalisa ta sahale wa Tinubu ya kashe N500bn don rage radadin cire tallafin mai

Sai dai Mr. Alake ya ce bayan da shirin ya sha suka daga ƴan ƙasa, shugaba Tinubu ya umarci jami’ansa su fito da tsarin da zai fi tasiri wurin ragewa al’umma raɗaɗin janye tallafin.

Ya kuma ce kafin akai ga fito da sabon tsarin, shugaba Tinubu ya bada umarnin raba takin zamani ga manoma miliyan 50 a faɗin Najeriya nan take.