✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cire tallafin man fetur alheri ne ga Najeriya — Ministan Labarai

Da ba a cire tallafin man fetur ba sai lamarin ya muni fiye da yadda ake gani a yanzu.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris Malagi ya ce, cire tallafin man fetur shi ne mafi a’ala ga kasar nan.

A cewar ministan, ba don gwamnati ta cire tallafin man ba, da wahalar da ake ciki a ƙasar sai ta fi ta yanzu.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake kare matakin gwamnatin ƙasar na cire tallafin mai a yayin wata hira da tashar talabijin ta Channels.

“Eh tabbas mun yi hasashen cewa ‘yan Najeriya za su fuskanci wasu matsaloli saboda cire allafin mai, amma da ba a yi hakan ba sai lamarin ya muni fiye da yadda ake gani a yanzu.

“Da ba a cire tallafin man fetur ba, zai yi wahala a iya aiwatar da duk wani aiki da zai kawo ci gaba mai ma’ana a kasar.

“Gwamnatin Tinubu ta kudiri aniyar farfado da tattalin arzikin kasar don wannan matsala ba yanzu muka soma fuskantarta ba.

“Saboda haka yana da kyau ’yan Najeriya su lura cewa gwamnatin Shugaba Tinubu tana da jan aiki a gabanta, shi ya sa tun daga hawansa ya sanar da cewa dole ne biyan tallafin man fetur ya zama tarihi.

“Muna ci gaba da daukan matakin da ya dace musamman a kan matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki.

Ana iya tuna cewa, a jawabinsa na farko bayan rantsuwar karbar mulki a watan Mayu na 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu sauran tallafin mai.

Tun daga wannan sanarwar ce kayayyaki da sauran harkokin rayuwa a Najeriya suke ta tashin gwauron zabo, rayuwa take ta kara tsada ga jama’a.

Kafin cire tallafin man ana sayar da lita ɗaya a kan naira 189 a watan Mayu, amma bayan sanar da cire tallafin man fetur din farashin ya koma daga naira 650 zuwa sama.