✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za a dawo da tallafin man fetur ba — Minista

Ministan ya ce sauye-sauyen da Tinubu ya ɓullo da su, na kawo sakamako mai kyau.

Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta soke sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya kawo a ɓangaren canjin Dala da kuma ɓangaren man fetur ba.

Edun, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi sabuwar Ƙaramar Ministar Kuɗi, Doris Uzoka Anite, a hedikwatar ma’aikatar a ranar Litinin.

Ya ce, “Yanzu Najeriya tana da farashin dala wanda yake tafiya daidai a kasuwa, da kuma kasuwar mai wacce aka sauya mata fasali.

“Waɗannan sauye-sauye ne da ya kamata a yi shekaru da dama da suka gabata, amma Shugaba Tinubu ne ya fara aiwatar da su.”

Edun, ya ƙara da cewa, a matsayinsa na ministan da ke kula da tattalin arziƙi, yana da muradin ganin an ci gaba da aiwatar da waɗannan sauye-sauye don rage talauci.

Ya kuma yi maraba da goyon bayan sabuwar ministar da aka naɗa wajen cimma manufofin.

Ya ƙara da cewa, aiki tare da ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu yana da matuƙar muhimmanci don samun nasarar aiwatar da sauye-sauyen.

Har ila yau, ya bayyana cewa manufofin tattalin arziƙin da ake aiwatarwa a yanzu suna haifar da ɗa mai ido.

A martaninta, ƙaramar ministar ta jadadda aniyarta na yin aiki tare da dukkanin masu ruwa da tsaki don bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.