Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce bai yi nadamar cire tallafin man fetur ba, duk da matsin tattalin arziƙi da Najeriya ke fuskanta.
A yayin wata hira da manema labarai a Jihar Legas, Tinubu ya bayyana cewa, cire tallafin fetur, ita ce kawai hanyar da za ta kai Najeriya gaci.
- Najeriya na kan turbar samun ci gaba mai ɗorewa — Tinubu
- Majalisar dokokin Filato ta amince da kasafin kuɗin 2025
“Lamarin ba mai sauƙi ba ne, amma ya zama dole don makomar ƙasar nan.”
Ya ƙara da cewa ya yanke wannan shawarar ne domin tabbatar da an samu kyakkyawar rayuwa a nan gaba
“Muna nema wa ’ya’yanmu da jikokinmu kyakkyawar makoma. Wannan yana da nasaba da gina ƙasar nan.”
A watan Mayun 2023, Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a lokacin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban ƙasa, bayan ya gaji Muhammadu Buhari.
Wannan matakin ya haifar da tashin farashin kayan masarufi, wanda ya jefa mutane da dama cikin wahala tare da ƙaruwar farashin rayuwa.
“Na san wahalar da wannan mataki ya haifar, amma nan da wani lokaci, zai amfanar da mu,” in ji Tinubu.
“Ba za mu iya ci gaba da dogaro da tallafin da ke laƙume albarkatunmu ba.”
Duk da cewa mutane da dama a Najeriya sun fuskanci wahala tun bayan cire tallafin, Tinubu ya kafe kan matakin nasa.
“Wannan mataki yana da wuya, amma ya zama dole domin ci gabanmu. Dole ne mu yi zaɓi mai wahala don amfanin ƙasar nan.”
Har ila yau, ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kan wasu shirye-shirye don rage tasirin cire tallafin, ciki har da tallafa wa al’umma da hanyoyin da za su dogara da kansu.
Duk da ƙalubalen, Shugaba Tinubu yana ganin cewa ƙasar za ta amfana a nan gaba.
Ya jaddada cewar cire tallafin man fetur ɗin wani muhimmin mataki ne don samun tattalin arziƙi mai ɗorewa da ci gaba.
“Idan lokacin ya zo, ’yan Najeriya za su ga fa’idar wannan mataki,” in ji shi.