Asusun Lamuni na Duniya, IMF ya ce ba shi da hannu a cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Najeriya .
IMF ya ce Tinubu gaban kansa ya yi wajen cire tallafin mai amma asusun bai ba shi shawarar yin hakan ba.
- Gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Kano neman tashin hankali ne — APC
- Zaɓen Ƙananan Hukumomi: An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a Kano
Wannan dai na ɗauke a wata hira da darektar IMF a nahiyar Afirka, Abebe Selassie ta yi da manema labarai a birnin Washington na Amurka a ranar Juma’a.
“Shawarar cire tallafin mai daga cikin gida ne. Shugaba Tinubu ne ya yi. Ba mu da shirye-shirye a Najeriya. Damar da muke da ita ba ta wuce tattaunawa ba, kamar yadda muke yi da sauran ƙasashe kamar Japan da Birtaniya.”
Sai dai Selassie ta jaddada cewa shawarar da Gwamnatin Tinubu ta ɗauka dangane da cire tallafin man fetur ɗin na ɗaya daga cikin dabarun samar da bunƙasa tattalin arziki mai ɗorewa a Nijeriya.
Ana iya tuna cewa, a ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne dai Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai jim kaɗan bayan rantsar da shi tun ma kafin ya shiga ofis.
Tun bayan sanar da cire tallafin man fetur ɗin farashin litar mai ta riƙa hauhawa inda a yanzu ake sayarwa kan kusan N1200 a sassan ƙasar.
Masu lura da al’amura dai ba su ɗora laifin cire tallafin mai da Tinubu ya yi a kan IMF ba kasancewar ya yi hakan ne tun kafin ya shiga ofis.
Sai dai galibi ’yan Najeriya sun fi alaƙanta cire tallafin man fetur ɗin da kuma na wutar lantarki da Tinubu ya yi da asusun na IMF.