✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da ni ne mulki a Najeriya da ba ta shiga tasku ba — Atiku

Atiku ya ce manufofin da Tinubu ke bijiro da su, na ƙara jefa 'yan Najeriya cikin ƙangin talauci.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce manufofin da Shugaba Tinubu ke bijiro da su, ba su da kan gado. 

Ya ce Gwamnatin Tarayya na bijiro da manufofin tattalin arziƙi waɗanda ba su da ma’ana kuma na ƙara jefa ’yan Najeriya cikin wahala.

“Yin sauye-sauye don daidaita farashin canjin kuɗi, kuɗin wutar lantarki, da farashin man fetur lokaci guda, wannan matakai sun yi tsauri a lokaci guda,” in ji shi.

Atiku, ya bayyana cewa da shi ne shugaban ƙasa, zai bi abubuwa a hankali don rage raɗaɗin da sauye-sauye za su haifar.

Atiku ya ce ba zai cire tallafin mai ko ƙara kuɗin wutar lantarki a lokaci guda ba.

Ya bayar da misalin da ƙasashen Malaysia da Indonesia, inda aka cire tallafin mai a hankali don bai wa mutane lokaci su saba.

Hakazalika, Atiku ya nuna muhimmancin tuntuɓar masu ruwa da tsaki kafin fara aiwatar da manyan sauye-sauye a ƙasar nan.

Ya ce, “Da mun tsara abubuwa da kyau kuma cikin tsanaki; tafiyata ta yi gyare-gyare wanda za a amfana da su ta hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki.”

Ya kuma ce manufofinsa za su mayar da hankali wajen bunƙasa tattalin arziƙi da tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa.

Ya bayar da shawarar kafa Asusun Tallafa wa Tattalin Arziƙi na dala biliyan 10 domin taimaka wa ƙananan masana’antu, tare da shirye-shiryen samar wa matasa ayyukan yi.

Atiku, ya kuma ce zai mayar da hankali wajen yaƙi da cin hanci, musamman a ɓangaren albarkatun mai, tare da gyara matatun mai ka cikin gida domin rage dogaro da shigo da mai daga waje.

Har ila yau, ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen ba wa marasa galihu tallafin da zai taimaka musu don sabawa da sauye-sauyen tattalin arziƙi.

A gefe guda kuma, ya yi alƙawarin cewa zai bunƙasa tattalin arziki ta yadda zai taimaka wa mutane, maimakon ƙara jefa su cikin ƙangin talauci da wahala.