Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammed Sani Yahya Jingir ya bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo wa al’ummar Nijeriya tallafin mai da gwamnatinsa ta cire.
Sheikh Jingir ya bayyana wannan bukata ce a lokacin da yake gabatar da nasiha, a wajen wa’azin Kasa da Kungiyar ta gudanar a karshen makon da ya gabata a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ya ce, “Shugaban Kasa don girman Allah ka dawo wa al’ummar Nijeriya, tallafin mai da aka cire, domin mu samu sassaucin matsanancin rayuwar da muke ciki a Nijeriya.”
Ya ce, “ana gaya mana cewa, an tara Naira tiriliyon 3 sakamakon cire wannan tallafin mai.
“A yayin da za a samu mutum daya a cikin barayin Nijeriya, wanda zai saci sama da waɗannan kuɗaɗe a lokaci guda.
“Ya kamata gwamnati ta kama masu sace kuɗaɗen Nijeriya, ta dawo mana da tallafin man da ta cire.
“Na haɗa Shugaban Kasa Tinubu da sunan Allah ka dawo wa al’ummar Nijeriya tallafin mai da ka cire.
“Na kusa da Shugaban Kasa Tinubu, ku gaya masa ya dawo mana da tallafin man fetur.
“Domin mu samu sassaucin matsanancin rayuwar da muke ciki a Najeriya”.
Sheikh Jingir ya yi bayanin cewa, Allah ya albarkaci Arewacin Nijeriya da filayen noma da dausayi.
Don haka, ya yi kira ga Ministan Gona ya yi hanyar da za a sami taki da iri da sauran kayan aikin noma a cikin sauki.
Ya ce, babu shakka idan aka samar da kayan aikin noma, za a ga irin ɗimbin noman da manoman Nijeriya za su yi.