Iyalai da dangin wadanda suka rasu a lokacin ambaliyar ruwa da ta faru a kananan hukumomin Suleja da Tafa da ke Jihar Neja sun yi korafi a kan yadda Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ta raba tallafin kudi da na kaya ga wadansu daga cikinsu, yayin da wadansu kuma suka yi zargin cewa ba a ba su komai ba.
A ranar Larabar makon jiya ne hukumar ta raba tallafin kudi da kayan abinci da kayan gini ga wadansu da lamarin ya shafa a ranar 9 ga Yuli inda aka rasa rayukan mutum 15 da rushewar gidaje sama da 100 a kananan hukummin biyu. Haka ma wadansu daga cikin wadanda suka samu taimakon sun yi korafin cewa abin da aka ba su ya gaza wanda hukumar ta sanar cewa ta bayar.
Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa wanda ya rasa iyali 8 a yayin ambaliyar, Malam Sa’adu Abubakar Asha ya ce ya yi ta samun kira ta waya daga jama’a bayan wani labari da aka ruwaito hukumar tana cewa an ba shi Naira miliyan 4, alhali Naira dubu 200 ne hukumar ta ba shi, kuma ba ta sanar da shi cewa akwai karin kudi da za ba shi a nan gaba ba.
Sauran wadanda suka koka sun hada da iyalin wani matashi da ya rasu a ambaliyar mai suna Idris Faruk inda dan uwansa Alhaji Musa Sahabi ya ce iyalansu sun halarci wajen rabon tallafin amma ba a su komai ba. Sai wadanda gidajensu ko wuraren sana’arsu suka rushe sakamakon ambaliyar.
Da aka tuntubi Babban Daraktan Hukumar SEMA, Malam Ahmad Ibrahim Inga, ya ce hukumar na jiran wasu kudade daga Ma’aikatar Kudi ta Jihar ce don karasa aikin rabon, inda ya ce daga cikin Naira miliyan 30 da gwamnatin jihar ta sanar cewa za a raba wa mutanen da lamarin ya shafa, akwai Naira miliyan bakwai da za a bai wa iyalan mutum 14 da aka tabbatar sun rasu a ambaliyar. Ya ce za a ba da Naira dubu dari biyar a kan kowane mammaci daya.