Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gargadi ’yan kasar da su yi hattara da ’yan damfara masu cewa ya wakilta kan shirinsa na bayar da tallafi.
Mukaddashin Jami’in Hulda da Jama’a na CBN, Osita Nwanisobi a cikin wata sanarwa ya bukaci ’yan Najeriya da su gudi masu danfara na intanet da ke kirkirar shafukan bayar da tallafi da sunan bankin.
Nwanisobi ya ce bankin na da shirye-shiryen tallafi da dama amma kuma tattaunawa kai tsaye da masu neman tallafin ba ya daga cikin tsarinsa.
Ya ce dole ne duk mai neman tallafi ko rance daga bankin ya bi tsare-tsaren bankin kuma babu wani mutum da ke da tabbacin kai tsaye na samun tallafin da CBN ke ba wa ’yan Najeriya.
Don haka ya bukaci ’yan kasa da su guji biyan kudade ga kamfanoni ko kungiyoyi masu cewa bankin ya wakilta kan shirin ba da rance ko tallafin COVID-19.
Ya bukaci matasa da masu kananan sana’o’i da su yi watsi da sakonnin da ke yawo a shafukan zumunta cewa CBN za ta bayar da rance ko tallafi.
Sanarwar ta nanata cewa babu wani kamfani da bankin ya nada ko ya tantance a matsayin wakili ko ejan dinsa a wani shirinsa na bayar da tallafi.