’Yan kasuwa da kananan ’yan tireda a kasuwanni da sauran sannan birnin Kabul na kasar Afghanistan sun ci gaba da gudanar da harkokinsu bayan kungiyar Taliban ta kwace mulki.
’Yan kasuwar sun shaida wa gidan talabijin na kasar China CCTV cewa da farko sun dauka za a yi kashe-kashe idan Taliban ta kwace mulki amma komai ya daidaita, a yayin Gwamnatin Taliban ke fito da wasu manufofinta.
Duk da haka wasu ba su saki jiki ba, ganin an saki fursunoni daga gidajen yari a fadin kasar, akwai kuma masu ganin Gwamnatin Taliban ba za ta cika alkawuran da ta dauka na ba wa mata hakkokinsu da kare mutanen kasar da kuma yafiya ga wadanda suka yake ta ba.
Amma wani mazaunin birnin Kabul, Nasir Ahmad ya ce, “Ina fata gamnatain za ta ajiye makamai domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali domin ci gaban al’ummar Afghanistan baki daya.”
Taliban za ta binciki mayakanta
A nata bangaren, Taliban, wadda ke fito da wasu manufofinta daidaita kasar ta yi alkawarin bincikar duk dan kungiyar da mutanen kasar suka yi korafi a kansa kan gallaza musu.
Ta bayar da wannan sanarwar ce bayan da ta umarci duk fararen hulan kasar da su mika makamansu daga wasu jami’anta da ta ayyana.
Sanarwar ta ce duk mamban Taliban da aka samu korafi a kansa, za a gaggauta gudanar da cikakken zuzzurfan bincike a kansa.
Wani jami’in gwamnatin ta Taliban ya ce kada ’yan Taliban su dauka nasarar da suka samu ta ba su damar yin duk abin da suka ga dama, su fahimci cewa nasarar ta mutanen Afghanistan ne gaba daya.
Sun kuma yi alkawarin tattaunawar zaman lafiya da jami’an tsohuwar gwamnatin Shugaba Ashraf Ghani, wanda ya tsere zuwa birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Kungiyar ta bayyana cewa sabanin salon mulkinsu na baya da shugabanninsu suke boye, yanzu shugabanninsu za su rika fitowa fili.
“A hankali duniya za ta ga shugabanninmu, babu wani boye-boye,” kamar yadda babban jami’in Taliban din ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Birtaniya za ta tsugunar da ’yan Afghanistan
Birtaniya ta ce za ta tsugunar da dubban ’yan Afghanistan da suka yi aiki tare da sojojinta a kasarsu, domin gudun hari daga Taliban.
Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ta ce ma’aikata 5,000 ne za su shigo a wanan shekarar, amma adadin zai iya ninkawa zuwa 10,000.
Akwai kuma fararen hula 20,000 da za a ba wa damar shigowa domin zaman gudun hijira a Birtaniyar.
Sakatare Harkokin Wajen Birtaniya, Priti Patel ta ce ba a lokaci guda kasar za ta karbi mutanen ba, kuma za a bi matakai domin tantance bakin haure da halastattun ’yan gudun hijira da za su shigo Birtaniya.
A cewarta, a yayin da suke tattaunawa da Ma’aikatar Tsaro kan lamarin, a halin yanzu sun fi mayar da hankali wajen kwaso mata da ’yan mata da kuma mutanen da suka fito daga kabilu marasa rinjaye zuwa kasar.
Ma’aikatar ta yi zargin cewa tana da hujjoji na bidiyoyi da ke nuna Taliban na kai hari kan sojoji da jami’an tsohuwar gwamnatin kasar.
Hakan nan zuwa ne a yayin Shugaban Amurka, Joe Biden da takwaransa na Birtaniya, Boris Johnson suka tattauna kan halin da ake ciki a kasar ta Afghanistan.