Asibitin Kasa da ke Abuja ya ce takardar rashin lafiyar da dakataccen shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimin Gado ya gabatar wa Majalisar Dokokin Jihar Kano kan lafiyarsa ta bogi ce.
A cikin wata amsar wasika da asibitin ya aike wa Majalisar dauke da kwanan watan 19 ga watan Yulin 2021, wacce Darakatan Sashen Kula da Gwaje-gwajen asibitin, Dokta A. A. Umar ya sanya wa hannu, asibitin ya ce ya binciki takardun kuma ya gano na bogi ne.
- Babu yarjejeniyar Buhari zai mika wa Tinubu mulki a 2023 – Okechukwu
- ’Yan sa kai za su fara jagorancin yaki da ’yan bindiga a Sakkwato – Tambuwal
“Bayan bukatar da ku ka gabatar mana da kuma binciken da muka yi a kan haka, muna son mu shaida muku abin da muka gano. Cewa ba mu da bayanan wani mara lafiya mai suna Muhuyi Magaji a asibitinmu, kuma babu wani fayil da aka bude da wannan sunan,” inji wasikar.
Tun da farko dai Majalisar Jihar ta aike da goron gayyata ga Muhuyin kan ya bayyana a gaban kwamitin da ta kafa don binciken zarge-zargen da ake masa ranar Laraba, 14 ga watan Yulin 2021.
To sai dai ya gaza bayyana a gaban kwamitin inda ya fake da cewa ba shi da lafiya har ma ya hada da kwafin takardun asibitin na kasa, wanda hakan ne ya sa majalisar ta nemi tabbatar da sahihancin takardar daga asibitin.
Kazalika, asibitin ba wai kawai ya bayyana cewa takardar ta bogi ba ce, ya kuma ce ba shi da kowanne irin bayanai a karkashinsa dauke da sunan Muhuyin.
“A bisa bincikenmu, babu wani ma’aikacin asibitinmu mai suna Dokta Bayo ko sahannunsa.
“Tuni muka daina rubuta sakamakon gwaje-gwaje a takarda muka koma aikewa da su ta na’ura mai kwakwalwa.
“Saboda haka, takardar da kuka aiko da kwafinta ba sahihiya ba ce,” inji asibitin.
Ana sa ran nan ba da jimawa ba dai kwamitin majalisar zai gabatar da rahotonsa ga gwamnatin Jihar.
A farkon watan Yuli ne dai Majalisar ta dakatar da Muhuyi daga shugabancin hukumar saboda zargin aikata ba daidai ba, biyo bayan wata takun saka tsakaninsa da gwanatin Jihar saboda kin karbar wani ma’aikacin da ta tura hukumarsa.
Daga bisani kuma an maye gurbinsa da Barista Mahmoud Balarabe a matsayin shugaban hukumar na rikon kwarya.