A watan Azumin Ramadan mai kamawa limamai shida ne Gwamnatin Kasar Saudiyya ta ayyana domin jagorantar sallolin Tarawih da Tahajjud a Masallacin Haramin Makkah.
Ga muhimman abubuwan da muka rairayo muku a takaice game da limanan sallolin na Kiyamullaili:
- Fuskokin Limaman Sallar Tarawih da Tahajjud a Makkah
- An yi jana’izar tsohon Limamin Masallacin Harami, Sheikh Al-Sabuni
- Za a gwangwaje malamai da kyautar motoci
- Sheik Abdul Rahman Al-Sudais
- Sheikh Sudais shi ne babban Limamin Masallacin Haramin Makkah
- Shi ne kuma Shugaban Hukumar Gudanarwar Masallatan Haramin Makkah da Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina.
- An haife shi ranar 10 ga watan Fabrairu, 1960 a Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya
- Yana da mata daya, sunanta Fahda Ali-Raouf kuma Allah Ya azurata shi da da daya, Abdullah bin Abdul Rahman Al-Sudais.
- Sheikh Saud Al Shuraim
- Sheikh Shuraim Farfesa ne a Fannin Shari’a da Darussan Musulunci a Jami’ar Umm Al-Kura da ke garin Makkah.
- Baya ga kasancewarsa gangaran a haddar Al-Kur’ani, Sheikh Shuraim mai aikin yada da’awar Musulunci ne
- An haife shi a ranar 19 ga Janairu, 1964, a birnin Riyadh, kasar Saudiyya
- Ya kammala giriinsa na farko a Jami’ar Umm Al-Kura a 1995
- Yana daya daga cikin manyan limaman Sallar Juma’a a Masallacin Haramin Makkah
- Sunansa na ainihi Saud ibn Ibrahim ibn Muhammad Al-Shuraim.
- Abdullah Awad Al Juhany
- An haifi Sheikh Juhany ranar 13, ga watan Janairu 1976, (Shekaru 45), a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.
- Ya yi digirinsa na farko a kan Ilimin Al-Kur’ani Mai Girma a Jami’ar Musulunci da ke Madina, digirinsa na uku kuma a Jami’ar Ummul Kura da ke Makkah.
- Sheikh Juhany daya ne daga cikin manyan Limamai a Masallacin Haramin Makkah Mai Alfarma.
- Maher Al Mueaqly
- An haifi Sheikh Maher Al Mueaqly ranar , ga Janairu, 1969 a birnin Madina
- Sunan mahaifiyarsa Sa’imah bint Mahmud Al-Sisi, mahaifinsa kuma Hamad Bin Muiqal Al Muaiqly
- Yana daga cikin manyan limamai a Masallacin Haramin Makkah da Masallacin Madina
- Sheikh Bandar Baleelah
- Haifaffen birnin Makkah ne a 1975
- Sunansa Bandar bin Abdulaziz bin Siraj bin Abdul Malik Baleelah
- Ya yi digirinsa na farko a Makkah, inda ya kammala a 1996
- Ya kammala Digirinsa na biyu a Jami’ar Ummul Kura a 2002
- Digirinsa na uku kuma a 2008 a Jami’ar Musulunci da ke Madina
- Ya zama limamin wucin-gadi mai jagoranci Sallar Tarawih a Masallacin Haramin Makkah a watan Ramadan, shekarar 2013.
- Cikin wata uku kuma ya zama Babban Limami cikakke a masallacin
- Sheikh Bandar, Farfesa ne a Tsangayar Shari’ah a Jami’ar Da’if
- Sheikh Bandar ya wallafa littafi kan Sallar Rokon Ruwa a 2016
- Yasser Al-Dosari
- Sunansa Yasser Ibn Rashed Ibn Houseine Al Ouadaani Al Dossari
- An haife shi a 1980 a unguwar Al-Kharj da ke Riyadh a Saudiyya
- Ya yi karatu a Jami’ar Musulunci ta Imam Muhammad Ibn Saud da ke birnin Riyadh