Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da tsige Sarkin Zurmi Alhaji Atiku Abubakar tare da Sarkin Dansadau Alhaji Hussaini Umar daga mukamansu kan zargin taimaka wa ayyukan ’yan bindiga a yankunansu.
Har wa yau gwamnatin jihar ta tsige Hakimin Birnin Tsaba, Alhaji Sulaiman Ibrahim Danyabi daga mukaminsa.
- Katsina: Masari ya nada Muntari Lawal Sakataren Gwamnati
- Daren Lailatun Kadar da ayyukan 10 na karshen Ramadan
Hakan ya biyo bayan shawarar da aka yanke a zaman Majalisar Zartarwar jihar, wanda Mukaddashin Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Hassan Mohammed Nasiha Gusau ya jagoranta.
Kwamishinan yada labaran jihar, Ibrahim Magaji Dosara ne ya sanar da hukuncin ga manema labarai a ranar Laraba, a Gusau.
Majalisar ta amince da shawarar kwamitin mutum shida da gwamnatin jihar ta kafa, domin duba rahoton da suka gabatar kan binciken yadda sarakunan gargajiyar uku ke da hannu wajen taimaka wa ayyukan ’yan bindiga a jihar.
Gwamnatin jihar ta dakatar da sarakunan a bayan kan yadda aka dinga zargin su da taimaka wa ayyukan ’yan bindiga a yankunansu.
Sakamakon binciken kwamitocin ya nuna yadda sarakunan ke yin sama da fadj da filayen mutane a yankunansu, wanda gwamnatin jihar ta bayar da umarnin a mayar wa wadanda aka karbe musu filayensu ba bisa ka’ida ba.