✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tabbas za mu ba matasa tallafin Naira 5,000 – Jam’iyyar APC

A makon da ya gabata ne ’yan majalisar… daga bangaren APC su ka yi fatali da kudurin  bai wa matasa marasa aikin yi Naira dubu…

A makon da ya gabata ne ’yan majalisar… daga bangaren APC su ka yi fatali da kudurin  bai wa matasa marasa aikin yi Naira dubu biyar-biyar a duk wata, da takororinsu na jam’iyyar PDP suka gabatar, kamar yadda jam’iyyar APC ta yi alkawarin yi a yayin takarar zabe. Sai dai bayan al’amarin wanda a ke ganin tamkar rufa asiri ne da ’yan majalisar suka yi adaidai lokacin da takwarorinsu na jam’iyyar adawa ke neman tona masu shi, jam’iyyar ta bakin kakakinta Alhaji Lai Muhammad ta bayyana cewa shirin aiwatar da tsarin na nan daram. Aminiya ta zanta da shugaban matasa na jam’iyyar Ibrahim Dasuki Jalo a kan al’amarin. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Da farko sai ka gabatar mana da kanka.
Ibrahim D Jalo: Sunana Honorabul Ibrahim Dasuki Jalo, ni ne shugaban matasa na jam’iyyar APC na kasa.
Aminiya: Bayan ’yan majalisa na APC sun nuna rashin amincewarsu a kan kudurin bai wa matasa tallafin Naira dubu biyar-biyar  a kowane wata, Jam’yyar APC ta bakin kakakinta Alhaji Lai Muhammad, ta bayyana cewa tana nan a kan bakanta na ganin an aiwatar da tsarin kamar yadda ta yi alkawari a lokacin zabe, shin wace hanya jamiyyar take ganin za a bi wajen samar da wannan kudin ganin yadda gwamnatin Buhari  take ta kukan rashin kudi a yanzu?
Ibrahim D Jalo: Alhamdulillahi, kamar yadda ka fada, maganar sama wa matasa marasa aikin yi ’yan wasu kudi kamar yadda ka ji jamiyya ta fada, tana cikin alkawura da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a lokacin gwagwarmayar neman zabe, kuma kamar yadda ka ji an yi bayani, jamiyya ta fito karara ta shaida wa al’umma cewa lallai wannan niyya da aka yi tana nan ba a fasa ba.  kuma abubuwa da suka faru a lokacin zaman majalisa ina ganin akwai ’yan kura-kurai da aka samu, ko kuma watakila rashin fahimtar manufar jam’iyya ne a kan al’amarin. Idan ka tuna, ai kafin zuwan wannan gwamnati ta APC akwai wadansu kudade da ake bai wa matasa a jihohi da kuma a matakin gwanatin tarayya da ake kira “Sure-P’’, kodayake ban tsaya na yi bincike ba a kan al’amarin don tabbatar da ko ta wace hanya ce za a bi a yanzu wajen samar da kudin, amma dai kamar yadda ka ji jam’iyya ta jadda ta bakin Alhaji Lai Muhammad, to na tabbata shugaban kasa Muhammadu Buhari na da wannan niyya kuma insha Allahu za a yi shi nan ba da dadewa ba.
Aminiya:  Ta wace hanya za a bi wajen tattara sunayen matasan?
Ibrahim D Jalo: Alal hakika ba a bayyanar tsarin da za a bi ba har  zuwa yanzu, amma dai da zaran bayani ya zo gare mu a matsayinmu na shugaban matasa, za mu bi duk tsarin da jam’iyya ke bi wajen ganin abun ya kai ga jama’a. Kamar yadda kowa ya shaida, wannan gwamnatin ta canji ce, kuma ba wani abu ba ne canjin illa samar da dabarbaru na ganin al’umma sun ci moriyar gwamnati kamar yadda ya kamata, ba tare da wasu sun shiga hakkin wasu ba wajen almundahana da kuma wasoson kudin al’umma, ina tabbatar wa jama’a cewa za a yi tsari wanda al’umma da aka yi dominsu, musamman matasa sun ci gajiyar abun, kasancewar wannan  gwamnati babu wasa a cikin al’amarinta, idan ta kuduri aniyar aiwatar da wani abu, to za ta tabbata da cewa ta yi.
Aminiya: Har zuwa wane lokaci kake jin  matasa za su fara cin gajiyar wannan tsari?
Ibrahim D Jalo: Kamar yadda aka sani, a ranar Laraba din nan ne aka rantsar da ministoci tare da bayyana masu ma’aikatunsu, kuma ka san da su ne za a tsara wannan al’amari don ganin ba a samu cikas ba, ka ga ke nan za a saurara tukuna.
Aminiya: Jam’iyyar PDP na ganin kun fitar da wannan tsari ne don yaudara kawai, me za ka ce?
Ibrahim D Jalo: Kamar yadda ka ji jam’iyyamu ta APC ta jaddada, ta kuma bayyana cewa wannan alkawari ne da ta yi, ba za ta yi kasa a gwiwa ba, ai ka ga ke nan kamata ya yi a jira tukuna a ga kamun ludayin, in dai ba mummunan fata ta ake yi mana ba, amma mu kam muna da yakinin za a yi wannan abun.