Hukumar tsaro ta DSS ta tabbatar da gayyatar fitaccen malamin Musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Dokta Ahmad Gumi domin amsa tambayoyi.
Kakakin DSS, Peter Afunanya, ya ce Hukumar ta gayyaci shehin malamin ne domin masa tambayoyi, amma bai bayyana dalilin tambayoyin ba.
- Ana dab da fara cinikin filin jirgin saman Abuja, Kano da wasu guda 2
- ’Yan wasa 20 da ke sahun gaba wajen lashe kyautar Balon d’Or a bana
“Tabbas Hukumar ta gayyaci Sheikh Gumi kuma ba bakon abu ba ne don ta gayyaci wani mutum,” inji Afunanya.
Sai dai bai bayyana ko hukumar za ta saki malamin wanda kuma tsohon hafsan Sojin Kasan Najeriya ne ba a ranar Juma’a.
DSS ta gayyaci fitaccen malamin ne kwanaki kadan bayan ya yi zargi cewa wasu sojoji na hada baki da ’yan bindiga.
A lokacin hirarsa da gidan talabijin na ARISE ranar Laraba, Sheikh Gumi, ya ce babu yadda ’yan bindiga za su samu makaman da suke amfani da su, sai da hadin bakin baragurbin jami’an tsaro.
Washegari kuma, Alhamis, Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, ta yi masa gargadi cewa ya yi hattara da kalamansa.
A safiyar Juma’a mai magana da yawun Sheikh Gumi, wato Tukur Mamu ya sanar cewa DSS ta gayyaci malamin zuwa ofishinta da ke Kaduna.