Alhaji Muhammadu Gawo Filinge, ga duk mai sauraron wakokin gargajiya na Hausa na dauri, ba bako ba ne. Mawaki ne da ya rayu a kasar Nijar kuma ya shahara a fagen wakar Hausa.
Na fara jin muryar wakarsa ne tun 1974, lokacin ina aji biyu a firamare. Musamman mukan kewaye rediyo muna sauraren shirye-shirye da wakoki, inda wakokinsa suka kasance abin sanyawa a mafi yawan lokaci.
A rayuwata, na kuduri ganawa da shi ido-da-ido, amma ban samu cikar wannan buri ba, domin kuwa ko a cikin ’yan shekarun nan na yi kokarin yin tattaki har zuwa garinsu, domin tattaunawa da shi domin bugawa a jaridar Aminiya. Nan ma Allah bai nufa ba.
Ba zan mance ba, a shekarar 2006, na ziyarci birnin Yamai, Babban Birnin kasar Nijar, domin halartar taron kasa-da-kasa na Marubutan Hausa. Farkon abin da na fara tambayar wani abokinmu dan jarida, Sulaiman Rejeto shi ne, shin mawaki Mamman Gawo yana nan raye, kuma yaya zan yi in gana da shi? Sai ya sanar da ni cewa yana nan, amma garin Gawo akwai nisa daga Yamai.
Na yi kokarin ganin na samu koda yini daya in je Gawo, amma yanayin taron da muka kwashe kwanaki 8 ya hana. Don haka dole ta sanya na hakura, tare da alkawarin zan yi tafiyayya ta musamman domin dawowa Nijar, domin ganawa da shi. Ko a lokacin, Sulaiman sai da ya samo mani kaset-kaset guda biyu na wakokinsa.
A 2010 da 2012 ma na sake komawa Nijar, inda muka gudanar da tarukan marubuta a Maradi da Zinder. Na yi kokarin samun damar zuwa garin Gawo amma hakata ba ta cin ma ruwa ba. Har kuma a 2014, na sake komawa Yamai, duk da haka ban samu ganawa da Muhammadu Filinge ba. Haka Allah Ya kaddara, ga shi har Allah Ya amshi kayanSa.
Kamar yadda labari ya ishe ni, Allah Ya yi wa Alhaji Muhammadu Gawo Filinge rasuwa ne a ranar Lahadi 24 ga watan nan na Janairu da muke ciki. Allah Ya amshi ransa ne, yana da shekara 76 a duniya.
A nan Najeriya, an samu mutane da yawa da suka yi ta’aziyya ga mawakin, musamman ma masoya wakokinsa. Cikin irin wadannan masoya, Malam Ibrahim Sheme, fitaccen dan jarida kuma mawallafi, ya shiga turakarsa ta Facebook, inda ya rubuta dogon bayani, har ma ya zayyano wasu daga cikin muhimman wakokinsa, domin tunawa da shi.
Da yake sharhi game da wata daga cikin wakokinsa, Malam Ibrahim Sheme yana cewa:
“Alhaji Muhammadu ya taba yi wa Alhaji Mamman Shata raddi kan wakarsa ta “Kumbon Apollo Ilebin” inda Shata ya nuna farin ciki da sauka kan duniyar wata da wasu Amurkawa biyu, Neil Armstrong da Buzz Aldrin suka yi a ran 20 ga Yuli, 1969, bayan sun yi tafiya kan Kumbon Apollo 11, wanda shi ne na’ura ta farko da ta kai dan Adam kan duniyar wata.”
Sheme ya ci gaba da cewa: “Gawo Filinge ya nuna adawarsa kan wannan yunkuri na kimiyya da Gwamnatin Amurka ta yi. Ya yi gargadi kan a daina shiga samaniya saboda kada a jawo fushin Ubangiji kuma ya gargadi Amurka da Rasha kan gasar da suke yi ta shiga sararin samaniya. Ya ce ai gwamma su maida hankali ga aikin gona kurum.”
Ba nan dan jarida Sheme ya tsaya ba, sai da ya kawo wasu daga cikin baitocin wakar ta Muhammadu Gawo, kamar haka:
“Ga wani sashe na wakar ta Gawo Filinge, mai taken ‘Ya Rabbi Sarki Mai Jama’a Ka Taimake Mu Don Ranar Juma’a’ wadda ta kasance daya daga cikin fitattun wakokinsa. Na kawo ta don alhinin wannan rashi da muka yi na daya daga cikin manyan mawakan Hausa na gargajiya:
“Don Shata yai maganar Ilaben,
Ni ko da Tirezi nake magana,
Shata a Ingilishi yake,
Ni ko Mamman a Faranshi nake.
(’Yan Amshi): Ingilishi ruwan sanyi ga kishi
Mu Faranshi reza yanke wuya.
Ya Rabbi Sarki Mai Jama’a Ka Taimake Mu Don Ranar Juma’a.
To, za ni tambaya taro jama’a,
Ina da tambaya domin ni sani.
(’Yan Amshi): Mai tambaya duk ba shi bata,
Ai da tambaya ne za a sani.
Ya Rabbi Sarki Mai Jama’a Ka Taimake Mu Don Ranar Juma’a.
Shirin ga da nij ji Amirka sukai,
Na halba kumbo kai ga wata,
In shina da umfani mu jiya.
(’Yan Amshi): In shina da umfani su matsa,
In bai da umfani su bari,
Ba mu son suna sauka ga wata.
Ya Rabbi Sarki Mai Jama’a Ka Taimake Mu Don Ranar Juma’a.
Don na ga abin ga da sun ka nufa,
Yawan shirin ga da sun ka matsa,
Na halba kumbo kai ga wata,
Ya kai mutane can shi aza.
(’Yan Amshi): Su debo ruwan can kai ga wata,
Su kwaso reran kai ga wata,
Suna ta ginar ramu kan wata;
Su bar zage-zagen nan da yawa,
Kar su je su fado muna mu mace.
Ya Rabbi Sarki Mai Jama’a Ka Taimake Mu Don Ranar Juma’a.”
Baya ga Malam Ibrahim Sheme, an samu wasu masoyan Mamman Gawo, sun tofa nasu albarkacin bakunan, inda wani Bashiru Musa ya yi ta’aliki kan wakar nan, yana cewa: “Ba sauki ke nan tsakanin Ingilishi da Faranshi. Ruwan sanyi kuma ga kishi ai ba shi da bambanci da reza mai yanka wuya.”
Wata mai suna Aishatou Med kuwa addu’a ta yi masa da cewa: “Allah Ya rahma masa.” Inda shi kuma fitaccen dan fim din Hausa, Shehu Hassan Kano ya ce: “Allah Sarki! Mazan jiya, Allah Ya jikan shi!” Kamar yadda Auwal G. danbarno shi ma ya ce: “Allah Ya gafarta masa.”
Daga nan ne kuma Ibrahim Sheme ya dawo, inda ya kara bayani game da marigayin, yana cewa: “Wani abu da yawanci ba a sani ba shi ne, Muhammadu Gawo Filinge a da malamin allo ne kuma marubucin wakokin Hausa. Wani ne ya ba shi shawarar ya sa kalangu a kidan wata waka tasa da ya rubuta yana rerawa, domin yana ganin za ta fi karbuwa. Sai ya jaraba ya gani din, nan da nan ta karbu har aka kira shi a gidan rediyo ya buga ta.”
Shi kuwa Sani Mu’azu cewa ya yi: “Babu shakka an yi rashin wani fasihi wanda ya ba da gudumawa sosai don raya adabin Hausa. Babu yadda za a yi mutum ya yi magana a kan Gawo Filinge ba tare da kawo batun ’yan matan Gawo ba. Ita wakar tasa ma, yakan rubuta ta ne da muryar ’yan matan Gawo a cikinta don muryarsa ta samu wato salon daidaituwa da ta su. Allah Ya jikansa, Amin.”
Mu ma a nan babu wani abin da za mu ce da ya wuce – Allah Ya jikansa da rahama, mu kuma Ya kyautata tamu, idan namu lokacin ya zo.
Ta’aziyyar Mawaki Muhammadu Gawo Filinge
Alhaji Muhammadu Gawo Filinge, ga duk mai sauraron wakokin gargajiya na Hausa na dauri, ba bako ba ne. Mawaki ne da ya rayu a kasar…