Wani masanin halayyar dan Adam ya yi gargadi cewa matsalar ta’addanci da ake fam da ita a Arewacin Najeriya na iya kaiwa shekara 30 masu zuwa kafin a ga bayanta.
Farfesa Bello Ibrahim na Jami’ar Bayero ta Kano ya yi hasashen ne a lokacin da yake bayyana talauci da rashin nagartaccen ilimi a matsayin manyan sabubban matsalar a yankin.
- NAJERIYA A YAU: Karin Kudi: A kwai Yiwuwar Daliban Jami’ar Maiduguri Su Daina Karatu
- Ka janye kazafin da ka yi min ko mu hadu a kotu —Saraki ga Gwamnan Kwara
“Idan ba a magance manyan matsalolin nan biyu na talauci da jahilci ba, ayyukan ta’addanci da na ’yan bindiga za su iya ci gaba na tsawon shekara 20 zuwa 30 masu zuwa.
“Binciken da aka gudanar kan yi wa kananan yara adalci ya gano cewa matasa masu shekara 18 zuwa 25 ba sa sa zuwa makaranta musamman a jihohin Borno da Yobe.
“Don haka idan har irin wadannan matasa suka fada hannun bata-garin mutane, to za su iya dora su a kan mugunyar hanya,” in ji Farfesa Bello Ibrahim.
Ya bayyana hakan ne a taron cikar daliban ajin 2008 shekara 14 da kammala digirin farko A Sashen Nazarin Hallayar dan Adama na Jami’ar da ya gudana a Kano.
Tun da farko, shugaban tsoffin daliban, Sulaiman Aminu Abubakar, ya ce sun shirya taron bayan 14 ne domin sada zumunci da juna da kafa gidauniyar tallafa wa iyalan wadanda suka kwanta dama daga cikinsu da yin ayyukan bunkasa ilimi a Jihar Kano.
Ya ce, “Mun san ba kowace matsala ce dole gwamnati za ta magance ba, shi ya sa a matsayinmu na tsoffin dalibai da ke aiki a wurare daban-daban muka ga dacewar mu ba da tamu gudunmawar.
“Tsoffin dalibai na yin muhimman ayyuka a al’ummomin da makarantunsu suke, kuma akwai wurare da dama da za mu iya bayar da gudummawa a Kano.
“Muna fata a karshen wannan taron za mu tara abin da za mu aiwatar da akalla aiki daya a wata makarantar firamare ko sakandare ko ta gaba da su a jihar.”