Shugaban Kungiyar ’Yan A-waren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu ya sake gurfana a gaban babbar kotun tarayya domin ci gaban shari’ar tuhumar sa da cin amanar kasa.
Sai dai duk da umarnin da alkalin kotun, Binta Nyako, ta ba shi na ya sauya kayan da ke jikinsa kafin sake halartar zaman kotun, ya yi kunnen kashi.
- Zaluncin ’yan kasuwa ne ke kawo tsadar man fetur – Masu ababen hawa
- Ban ji dadin sanya hotona a labarin rikicin Kannywood ba – Rahama Sadau
A zaman da aka yi a ranar 18 ga watan Janairu, Mai shari’a Binta Nyako ta umarci hukumar tsaro ta DSS ta ba wa Nnamdi Kanu damar canza tufafinsa da kuma ganawa da iyalansa.
Umarnin ya biyo bayan korafin da lauyan da ke kare shi, Mike Ozekhome (SAN), ya yi cewa ana take hakkin wanda yake karewa ainda ake tsare da shi.
Ozekhome, ya bukaci kotun ta umarci DSS ta ba wa Kanu damar sauya kaya da kuma gudanar da addininsa a wurin da yake tsare.
Kanu dai na fuskantar tuhume-tuhume 15 kan cin amanar kasa da ta’addanci ga gwamnatin tarayyar Najeriya.
Alkalin kotun, Binta Nyako ta dage zaman kotun har zuwa ranar 8 ga watan Afrilu 2022, don ci gaba da shari’ar.