kungiyar Fulani Makiyaya ta kasa (Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria) ta yaba da kokarin gwamnatin tarayya wajen nada kwamitin da zai samar da makiyaya/mashaya da kuma samar da burtali ga shanu a cikin kasa don magance rigingimun da ke afkuwa tsakanin makiyaya da manoma a kasar nan.
kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wata takarda da ta raba ga manema labarai mai dauke da sa hannun babban Sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Baba Othman Ngelzerma.
kungiyar, karkashin shugabancin sabon shugabanta, Ardo Muhamamdu Kirowa ta tabbatar da cewa za ta yi aiki tukuru wajen ganin an tafiyar da shugabancin kungiyar cikin nasara tare da bayar da kulawa game da jin dadin ’ya’yan kungiyar.
A sakonsa a yayin tabbatar da shugabancin sababbin shugabannin kungiyar ta Miyatti Allah, Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi kira ga sababbin shugabannin kungiyar da su kawar da gaba da kiyayyar juna a tsakaninsu, a maimakon haka su yi aiki tukuru wajen magance matsalolin da ke damun ’ya’yan kungiyar.
Ta yaba wa gwamnatin tarayya kan kokarin tallafa wa makiyaya
kungiyar Fulani Makiyaya ta kasa (Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria) ta yaba da kokarin gwamnatin tarayya wajen nada kwamitin da zai samar da…