✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta tabbata Zidane ya bar Real Madrid

Ya yanke hukunci barin Real Madrid shekara daya kafin karewar kwantaraginsa.

Zinedine Zidane ya yanke hukuncin barin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wadda yake horaswa.

Kocin dan asalin kasar Faransa, ya kawo karshen zamansa a kungiyar a karo na biyu bayan shafe kakar wasanni ta bana ba tare da ya lashe wani kofi ba.

Tun kafin karewar kakar wasanni ta bana, Zidane ya bayyana cewa zai sauwaka wa Real Madrid wajen ci gabanta.

Zidane ya fuskaci matsaloli da dama a kungiyar, duba da yadda ’yan wasansa suka sha fama da shi a bana.

Sai dai ya yanke hukuncin barin Real Madrid duk da cewar yana da ragowar shekara daya a kwantaraginsa.