✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kashe jaririnta dan wata takwas a Ibonyi

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ebonyi tana tsare da Ahmed Ajibore da matarsa mai suna Chidinma da ke Layin Obubra, Abakalike tana masu bincike, sakamakon…

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ebonyi tana tsare da Ahmed Ajibore da matarsa mai suna Chidinma da ke Layin Obubra, Abakalike tana masu bincike, sakamakon zarginsu da ake yi, cewa mijin ya umarci matarsa ta makure dansu dan wata takwas da haihuwa mai suna Emmanuel har ya mutu.

Wata majiya da ke makwabtaka da magidantan wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce:  “Shi Ajibore ne da kansa ya umurci matar tasa Chdinma da ta makure yaron har sai ya mutu, hakan kuwa aka yi.”

Da take yi wa manema labarai karin bayani, Chidinma uwar yaro Emmauel ta ce Ahmed mijinta da dare ya ba ta Naira dubu 3 da wata guntuwar igiya, ya ce ta yi amfani da ita ta makure wuyan yaron har sai ya mutu.

Itama Lobely Nwode, ’yar uwar Chidinma da take bayar da shaida wurin ’yan sandan, ta ce: “Sabani suka samu tsakanin Ahmed Ajobore wanda shi makanike ne da ’yar uwar tata, shi yasa ya bayar da umurnin ta kashe yaron.”

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ebonyi  ASP Lobeth Odah, ta tabbatar da cewa wadanda ake zargin suna hannu, ana binciken su.