Wata mata ce ’yar asalin kasar Brazil ta yi wani abin al’ajabi da ya bar dimbin mutane cikin mamaki da ta’ajibi.
Matar mai shekara 19 a duniya ta haifi tagwaye amma kowa mahaifinsa daban.
- Kotun Koli ta yi watsi da batun tsayar da dan takarar shugaban kasar PDP daga Kudu
- Pantami ya nada Mahmoud na Labarina a matsayin jakada
Rahotanni daga bakin likitan matar sun ce ba a cika samun irin wannan lamari na aukuwa ba, kuma ba za a ce ba ya faruwa ba gaba daya.
Ita kanta matar ta girgiza bayan gano cewa tagwayen ba mahaifinsu daya ba, inda ta ce ba ta taba tsammanin hakan zai faru da ita ba.
Lamarin ya faru ne sakamakon tarawa da ta yi da maza biyu a ranar daya, kuma aka yi sa’a kowanensu ya zuba mata kwan daukar ciki a ranar, kamar yadda likitan ya yi hasashe.
Ta haifi tagwayen bayan rainon cikin na tsawon wata tara.
Matar ta fara tunanin hada yaran da mahaifinsu, wanda a wannan lokaci ne ta girgiza bayan sanar da ita sakamakon abin da ya faru.
Da fari ta je an yi musu gwajin kwayar hallita (DNA), inda a nan ne aka gano cewa daya daga cikin tagwayen kwayoyin halittarsa sun dace da wanda take zaton shi ne mahaifinsu.
“Na tuna cewa na sadu da wani, don haka sai na kira shi domin a yi gwajin kwayar hallita, abin mamaki daya daga cikin tagwayen ne kawai ya dace da kwayoyin halittarsa.
Ban taba tunanin haka za ta iya faruwa ba kuma tagwayen kamarsu daya,” ta bayyana wa manema labarai.
Rahotanni sun ce likitan matar ya bayyana cewa ta yi rainon cikin lafiya lau kuma tagwayen suna cikin koshin lafiya.
Matar dai ta fito ne daga Kudu maso Yammcin garin Goias na kasar Brazil, amma ba a bayyana sunanta ba.
Matar ta ce tuni daya daga cikin mazan da ta sadu da su, ya dauki dawainiyar dan aka gano shi ne mahaifinsa.
Dokta Tulio Jorge Franco, likitan matar ya bayyana wa manema labarai cewa “Yana da makukar wahala hakan ta faru idan kwayayen daga mahaifiya suka fito sakamakon haduwa da kwayayen maza mabambanta.
Yaran sun yi gadon halittar mahaifiyarsu, amma sun girma a mahaifa daban-daban ne.”
Ya kara da cewa “Irin wadannan al’amura 20 ne suka faru a fadin duniya kawo yanzu.
“Ana kiran wannan al’amari da ‘Heteropaternal superfecundation’.
“Wannan ya fi faruwa galibi a tsakanin dabbobi kamar shanu da maguna da karnuka.
“Amma wannan al’amari bai cika faruwa a jinsin dan Adam ba, shi ya sa ya zama abin mamaki.”
Wannan al’amari ba kasafai ake samunsa ba, sai idan maniyyin namiji ya rayu a cikin mace na tsawon kwanaki kadan ko macen ta samar da kwai biyu a lokaci daya.