Wata mata ta garzaya kotu a yankin Kubwa da ke Abuja inda ta nemi kotun ta kashe aurenta saboda gazawar mijinta wajen ciyar da ita yadda ya kamata.
Matar ta fada wa kotun cewa, bana shekara hudu kenan da aurensu, inda ta zargi maigidan nata da gazawa wajen samar da abinci da daukar sauran dawainiyar gida a shekaru biyun da suka gabata.
- An kashe ’yan Boko Haram 9 ta hanyar harbi da kibiya a Borno
- Hajjin bana: Rukunin karshe na Alhazan Kwara sun iso Najeriya
Matar ta ce, “Shekara biyu ke nan rabona da shi, kuma ba ya kula da ni yadda ya kamata. Ba zan iya ci gaba da hakurin haka ba.”
Don haka ta bukaci kotun ta raba auren nasu duk da mijin ba ya kusa, bisa dalilan rashin abinci da kulawa.
Bayanai sun nuna kotun dai ta aika wa mijin da sammaci har sau biyu amma ko daya daga ciki bai amsa ba.
Sai dai alkalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Adamu, ya bukaci a sake aika wa mijin da sammaci a karo na uku, kana ya dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Agustan 2022.
(NAN)